Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Kwara ta ayyana ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekara. Gwamnatin ta bukaci a yi wa jihar da Najeriya addu'ar samun zaman lafiya.
Hukumar zabe ta ƙasa mai zama kanta watau INEC ta ce zuwa yanzu ta karɓi buƙatun yi jam'iyyu rijista akalla 110, ta ce za ta fitar da sunayensu gaba ɗaya.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi kalamai masu zafi kan minisotcin da Shugaba Bola Tinubu ya nada a gwamnatinsa. Ya ce ba su da inganci.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya fito ya yi Allah wadai da kisan wasu matasa suka yi wa matafiya 'yan Kano. Ya aika da sakon ta'aziyyarsa ga Gwamna Abba Kabir.
An yi rashi na daya daga cikin tsofaffin gwamnonin Najeriya. Cornelius Olatunji Adebayo wanda ya taba zama tsohon gwamnan jihar Kwara ya yi bankwana da duniya.
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya bayyana cewa akwai yiwuwar zai fice daga jam'iyyar APC. Ya ce ya je tarurrukan 'yan hadaka.
Shugaban jam'iyyar SDP na kasa, Alhaji Shehu Gabam, ya yi fatali da batun dakatarwar da aka yi masa daga kan mukaminsa. Ya ce har yanzu shi ne shugaba.
Gwamnatin jihar Taraba ta musanta nada sabon mataimakin gwamna. Gwamnatin ta ce babu kamshin gaskiya a cikin jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta.
Iran ta sanar da cewa yakin da take yi da Israila ya zo karshe. Sanarwar na zuwa ne bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan an kwashe kwanaki 12 ana yaki.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari