Manyan Labarai A Yau
'Yan daba sun farmaki hedkwatar jam'iyyar SDP ta kasa a ranar Talata. 'Yan daban sun farmaki hedkwatar am'iyyar ne biyo bayan dakatar da shugaban jam'iyyar.
Hukumar FDA ta amince da lenacapavir, matsayin rigakafin HIV. Amma UNAIDS ta bukaci a rage farashinsa da ya kai $28,218 don ya isa ga duniya baki ɗaya.
Kasar Isra'ila ta ce za ta cigaba da kai hare hare zuwa Iran bayan cimma yarjejeniya a tsakaninsu. Isra'ila ta ce Iran ta karya yarjejeniya amma ta musa.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sake caccakar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ya bayyana cewa Allah ya kare shi daga annoba.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, da sauran manyan 'yan adawa sun zaɓi sabuwar jam'iyyar ADA.
Qatar ta yi Allah wadai da yunƙurin Iran na kai farmaki sansanin sojojin Amurka da ke ƙasarta, ta ce ta samu nasarar kakkabo makamin da aka harbo.
Kasar Iran ta kaddamar da harin ramuwar gayya kan sansanin sojojin Amurka da kasar Qatar. Iran ta kai farmakin ne da makami mai linzami bayan harin Amurka.
Kungiyar Northern Nigeri'as Progressive Youth Assembƙy ts shawarci mai girma Bola Tinubu ƴa zabi Sanata Barau a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2027.
Wasu 'yan bindiga da ba a san ko waye ba sun tare hanya a jihar Benue. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da fasinjojin da ke kan hanyar zuwa birnin Makurdi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari