Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gaji dumbin basussuka daga wajen gwamnatin da ta gabace shi da Godwin Obaseki.
Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano ta gamu da koma baya bayan wasu daga cikin mambobinta sun fice daga cikinta. Tsofaffin 'yan APC din sun koma NNPP.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana ada shugabannin addinai a fadarsa da je Abuja domin tattaunawa kan batun barazanar da Amurka ta yi wa Najeriya.
Sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya musanta rade-radin da cewa ya tsere zuwa Turkey saboda barazanar Donald Trump.
Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihohi 19 na Arewa, Joseph John Hayab, ya warware zare da abawa kan barazanar da Donald Trump ya yi wa Najeriya.
Am gudanar da wata zanga-zanga a wasu kauyukan jihar Katsina kan matsalar rashin tsaro. Mutanen dai sun fita kan tituna ne bayan hare-haren 'yan bindiga.
Shugaba Bola Tinubu da gwamnoni za su halarci taron Editoci na Najeriya karo na 21 a Abuja, inda za a tattauna kan dimokuradiyya, tsaro, da makomar kafafen labarai.
Bernard Doro, wanda shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada, ya kama aiki a matsayin sabon ministan harkokin jin kai da yaye talauci, ya dauki alkawari.
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya goyi bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump, kan kashe-kashen da ake yi a Najeriya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari