Manyan Labarai A Yau
Shugaban jam'iyyar ZLP, Dan Nwanyanwu, ya ja kunnen tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan fitowa takara a zaben shekarar 2027. Ya tuna masa baya.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya shigar da kara kan sanata mai wakiltar Kogi ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Natasha Akpoti.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce jita-jitar da ake yadawa a soshiyal midiya cewa an kama shi a Faransa ba gaskiya ba ne. Ya fadi masu yada jita-jitar.
Wata mata mai juna biyu, Aisha Najamu ta rasaranta saboda ma'aikacin asibiti ya ki yarda a tura masa kudin sanya iskar numfashi ta asusun banki a jihar Katsina.
Sanata Adams Oshimhole ya ba da labarin yadda aka yi amfani da cibiyoyin kudi irinsu Opay lokacin da yan damfara suka masa kutse a asusun bankinsa.
Daniel Bwala ya ce Tinubu yana naɗa mutane, ko da kuwa waɗanda suka taba saba masa ne, bisa darasin da ya koya daga mahaifiyarsa na zama mai yafiya
Sabon Ministan tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya sha alwashi kan tsaron Najeriya. Janar Christopher ya kuma yi godiya kan son da aka nuna masa.
Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Zamfara ta gamu da koma baya bayan wasu daga cikin 'yan majalisar da take da su sun yi murabus. Sun bayyana dalilansu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da janar Christopher Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan tsaro. Hakan na zuwa ne bayan majalisa ta amince da shi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari