NUC Ta Saki Sunayen Jami’o’in Bogi 58da ke Aiki a Najeriya, Ta Gargadi Dalibai

NUC Ta Saki Sunayen Jami’o’in Bogi 58da ke Aiki a Najeriya, Ta Gargadi Dalibai

Abuja - Hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC) ta fitar da gargaɗi mai tsauri ga jama'a game da wasu jami'o'in bogi 58 da ke aiki ba bisa ka'ida ba a fadin Najeriya.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Hukumar ta ce waɗannan makarantu ba su da izini kuma suna aiki ba tare da amincewar gwamnati ba, don haka suna jefa ɗalibai cikin haɗarin samun takardun digiri na bogi, marasa daraja.

Hukumar NUC ta ce akwai jami'o'i 58 na bogi da ke aiki ba bisa ka'ida ba a Najeriya
Shugaban hukumar NUC, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu yana jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja. Hoto: @OfficialNUC
Source: Twitter

NUC ta gargadi dalibai kan jami'o'in bogi

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizo na ma'aikatar ilimi ta tarayya, NUC ta bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Don kauce wa rudani, duk wanda ya yi karatu ko ya karɓi kowace takardar shaidar digiri daga ɗayan waɗannan makarantu da ke aiki ba bisa ka'ida ba, ya kuka da kansa."

Kara karanta wannan

Trump ya ce an masa makarkashiya bayan ya samu matsaloli 3 a taron UN

Hukumar ta tabbatar da cewa an sanar da hukumomin da ke da alhakin tabbatar da doka da oda game da wannan al’amari don ɗaukar matakin da ya dace.

Hakazalika, hukumar NUC ta ce akwai wasu jami'o'i takwas da yanzu haka take bincike kansu, bisa zargin suna gabatar da kwasa-kwasan digiri ba bisa ka'ida ba.

Sunayen jami’o’i 58 na bogi a Najeriya

A ƙasa akwai cikakken jerin makarantu 58 da hukumar NUC ta bayyana a matsayin jami'o'in bogi da ke aiki ba bisa ka'ida ba a Najeriya:

  1. Jami'ar Accountancy and Management Studies (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  2. Jami'ar Christians of Charity American University of Science and Technology, Nkpor, jihar Anambra ko duk sauran rassan ta.
  3. Jami'ar masana'antu, Yaba, Lagos ko duk sauran rassan ta.
  4. Jami'ar Applied Sciences and Management, Port Novo, Jamhuriyar Benin ko duk sauran rassan ta a Najeriya.
  5. Jami'ar Blacksmith, Akwa ko duk sauran rassan ta.
  6. Jami'ar Volta (VUC), HO, Volta Region, Ghana ko duk sauran rassan ta a Najeriya.
  7. Jami'ar Royal, Izhia, P.O. BOX 800, Abakaliki, jihar Ebonyi ko duk sauran rassan ta.
  8. Jami'ar Atlanta, Anyigba, jihar Kogi ko duk sauran rassan ta.
  9. Jami'ar United Christian, Macotis Campus, jihar Imo ko duk sauran rassan ta.
  10. Jami'ar United Nigeria (UNUC), Okija jihar Anambra ko duk sauran rassan ta.
  11. Jami'ar Samuel Ahmadu, Makurdi, jihar Benue ko duk sauran rassan ta.
  12. Jami'ar UNESCO, Ndoni, jihar Rivers ko duk sauran rassan ta.
  13. Jami'ar Saint Augustine (SAUT), Jos, jihar Plateau ko duk sauran rassan ta.
  14. Jami'ar The International, Missouri USA, cibiyoyin nazari na Kano da Legas ko duk sauran rassan ta a Najeriya.
  15. Jami'ar Collumbus, UK (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  16. Jami'ar Tiu International, UK (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  17. Jami'ar Pebbles, UK (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  18. Cibiyar Nazarin Waje ta London, UK (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  19. Jami'ar Pilgrims (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  20. Makarantar Kasuwanci ta Lobi, Makurdi, jihar Benue ko duk sauran rassan ta a Najeriya.
  21. Jami'ar West African Christian (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  22. Jami'ar Bolta University College, Aba ko duk sauran rassan ta a Najeriya.
  23. Jami'ar JBC Seminary Inc. (Jami'ar Wukari Jubilee) mai haramtaccen reshe a Kaduna.
  24. Jami'ar Western, Esie, jihar Kwara ko duk sauran rassan ta a Najeriya.
  25. Jami'ar St. Andrews University College, Abuja ko duk sauran rassan ta a Najeriya.
  26. EC-Council USA, mai cibiyar karatu a Ikeja,.
  27. Jami'ar Atlas, Ikot Udoso Uko, Uyo, jihar Akwa Ibom ko duk sauran rassan ta a Najeriya.
  28. Jami'ar Concept College/Universities (London) Ilorin ko duk sauran rassan ta a Najeriya.
  29. Jami'ar Halifax Gateway, Ikeja ko duk sauran rassan ta a Najeriya.
  30. Jami'ar Kingdom of Christ, Abuja ko duk sauran rassan ta.
  31. Jami'ar Acada, Akinlalu jihar Oyo ko duk sauran rassan ta.
  32. Jami'ar Filfom, Mbaise, jihar Imo ko duk sauran rassan ta.
  33. Jami'ar Houdegbe North American, mai rassa a Najeriya.
  34. Jami'ar Atlantic Intercontinental, Okija, jihar Anambra.
  35. Jami'ar Open International, Akure.
  36. Jami'ar Middle Belt (Jami'ar North Central) Otukpo.
  37. Jami'ar Lead Way, Ugheli, jihar Delta.
  38. Jami'ar Metro, Dutse/Bwari Abuja.
  39. Jami'ar Southend, Ngwuro Egeru (Afam) Ndoki, jihar Rivers.
  40. Jami'ar Olympic, Nsukka, Jihar Enugu.
  41. Kwalejin Magunguna ta Tarayya, Abuja.
  42. Jami'ar Temple, Abuja.
  43. Makarantar Kasuwanci ta Jami'ar Irish, London (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  44. Jami'ar fasaha ta NUT, Lafia, jihar Nasarawa.
  45. Jami'ar Accountancy and Management Studies, Mowe, Titin Lagos – Ibadan da kuma reshenta a 41, titin Ikorodu, Lagos.
  46. Jami'ar ilimi ta Wenneba Ghana (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  47. Jami'ar Cape Coast, Ghana (aiki a Najeriya).
  48. Jami'ar AUCD da ke Cotonou, Jamhuriyar Benin (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  49. Jami'ar Pacific Western, Denver Colorado, mai cibiyar nazari a Owerri.
  50. Jami'ar Evangel University of America and Chudick Management Academic, Lagos.
  51. Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta jihar Enugu (reshen Gboko).
  52. Cibiyar ilimi ta Career Light Resources, Jos.
  53. Jami'ar West Africa, Kwali, Abuja.
  54. Jami'ar Coastal, Iba Oku, jihar Akwa Ibom.
  55. Makarantar Kasuwanci ta Kaduna, Kaduna.
  56. Jami'ar Royal University of Theology, Minna, jihar Niger.
  57. Jami'ar West African Union, tare da haɗin gwiwar International Professional College of Administration, Science and Technology, Najeriya (a kowane wuri take aiki a Najeriya).
  58. Jami'ar Gospel Missionary Foundation (GMF), Theological, 165 Isolo road, Cele bus stop, Egbe Ikotun, Lagos.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatun ɗalibai 240 a jami'o'in a Najeriya

Hukumar NUC ta gargadi dalibai da su yi hattara da karbar takardar digiri daga wasu jami'o'in bogi 58 a Najeriya
Ginin hedikwatar hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC) da ke Abuja. Hoto: @OfficialNUC
Source: Twitter

Jami'o'in bogi 37 NUC ta gano a 2024

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NUC ta sanar da cewa jami'o'i 37 aka gano cewa suna gudanar da ayyuka ba tare da amincewar gwamnati ba a 2024.

Mukaddashin shugaban NUC, na wancan lokaci, Chris Maiyaki, ya ce hukumar ta kama wasu mutane da laifin gudanar da jami'o'in ba bisa ka'ida ba a sassan Najeriya.

Chris Maiyaki ya bayyana cewa NUC ta hada hannu da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) wajen dakile ayyukan haramtattun makarantu a kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com