Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanya dokar ta baci ta awa 24. Gwamnan ya sanya dokar ta bacin ne bayan an samu barkewar rikici.
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya fito ya yi magana kan shekarun da yake da su a duniya. Ya bayyana yadda yake gano shekarunsa.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya hango makomar jam'iyyar a zaben 2027. Ya bayyana cewa APC za ta yi nasara cikin sauki.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ziyarci Goodluck Jonathan. Atiku ya ziyarci tsohon shugaban kasar ne bayan ya dawo daga Guinea Bissau.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Plateau, Rufus Bature, ya yi magana kan dalilin da ya sa ba su yi maraba da Gwamna Caleb Mutfwang ba. Ya ce ba su san niyyarsa ba.
Yunkurin juyin mulki a Benin ya kara shiga jerin juyin mulki da dama da sojoji suka yi a kasashen Afrika. Legit Hausa ta yi bayani game da kasashe 8.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta ba tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, zabi kan ya shigo a cikinta ko kuma ya kama kansa.
Fadar shugaban kasa a Benin ta yi tsokaci kan yunkurin da sojoji suka yi na kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon. Ta ce sojojin ba su karbe iko a kasar ba.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya fasa kwai kan matsalar garkuwa da mutane da ake fama da ita. Ya nuna yatsa ga 'yan siyasa masu neman mulki.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari