Manyan Labarai A Yau
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Zamfara. Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutum daya tare da yin awon gaba da wasu mutane.
Tsohon hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Babafemi Ojudu ya ce zai gayyaci Tinubu da Aisha Buhari zuwa wurin kaddamar littafin abin da ya faru a mulkin Buhari.
Iyalan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun bayyana adadin mutanen da suka amfana da koyarwar marigayin. Sun ce ya koyar da jama'a masu tarin yawa.
Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta gudanar da babban taronta na kasa. Jam'iyyar NNPP ta zabi Ahmed Ajuji a matsayin wanda zai ci gaba da jan ragamarta.
Allah ya yi wa shugaban masallacin Annoor da ke babban birnin tarayya Abuja rasuwa. Dr. Kabiru Kabo ya rasu ne a birnin Landan bayan ya dauki lokaci yana jinya.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sanya lokacin gudanar da babban taronta na kasa. APC ta shirya gudanar da taron ne domin zaben shugabanni a shekarar 2026.
Gwamna Babagana Umaru Zulum ya kaddamar da shirin koyar da matasa harkokin gyaran waya a Borno, sama da mutum 1,000 ne za su amfana da tallafin kudi.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi wa malaman makaranta babban gata. Gwamna Uba Sani ya tsawaita lokacin da za su yi ritayasu daga shekara 60.
Dan wasan tsakiya na Besiktas, Wilfred Ndidi, ya zama sabon kyafin din tawagar Super Eagles. Nadinsa na zuwa ne yayin da Najeriya za ta fafata a gasar AFCON.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari