Manyan Labarai A Yau
Hukumomi sun sanar da sakamakon zaben shugaban kasar Kamaru. Shugaba Paul Biya, ya doke abokin hamayyarsa, inda zai ci gaba da jan ragamar kasar.
Jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu, ya kasa fara kare kansa a gaban kotu kan zargin aikata ta'addanci. Ya ce babu wata tuhuma a kansa.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Farfesa Peter Umeadi ya fice daga jam'iyyar APGA kuma ya jingine siyaaa gaba daya, ya gode wa wadanda suka ba shi dama.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano, sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargin 'yan bindiga ne. An cafke su bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu.
Hukumar Hisbah ta samu nasarar dakile wani shirin gudanar da auren jinsi a Kano da wasu mutane suka shirya. An cafke mutanen da ake zargi akwai hannunsu.
Hadadden kwamitin majalisar dattawa da ta wakilai kan yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima, ya amince a kirkiro karin jihohi har guda shida a Najeriya.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan miyagun 'yan bindiga a jihar Kebbi. Sojojin sun hallaka 'yan bindiga masu yawa bayan an gwabza fada.
Jam'iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta yi watsi da batun amincewa da tsohon ministan harkoki na musamman, Kabiru Tanimu Turaki a matsayin dan takarar maslaha.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta sanar da soke batun auren shahararrun 'yan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya da Basira 'Yar Guda.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari