Jihar Legas
Hukumar kwastam ta kasa ta bayyana cewa zanga-zanga da ƴan Najeriya ke shirin gudanarwa ba za ta dakatar da Aikinta a tashar jirgin ruwan Apapa ba.
Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da shirye-shiryen fara gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya. An bayyana jerin wuraren da za a gudanar da ita.
Yan daba a jihar Legas sun fara gargadin mazauna jihar da su rufawa kansu asiri kar su fita zanga-zanga, tare da barazanar za su yi maganin duk wanda ya fito.
Olukoya Ogungbeje, wani lauya mazaunin Legas ya yi karar gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro kan zargin suna yunkurin hana zanga-zangar 'yunwa' a fadin kasar.
Matasa a jihar Legas sun nemi sauran takwarorinsu a kasar nan da su daina mararin fita zanga-zangar gama gari da aka shirya gudanarwa a ranar 1-10 Agusta, 2024.
Diyar Shugaba Bola Tinubu na Najeriya, Folashade Tinubu ta yi magana kan shirin da matasa ke yi a kasar inda ta ce shiga lamarin bai zai haifar da 'da mai ido ba.
Fitaccen mawaki Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya dira kan masu zanga-zanga inda ya ce talauci da rashin aiki ne yake saka matasan ke son fita.
Mawallafin jaridar Ovation, Mista Dele Momodu ya dora alhakin fita zanga zanga da jama'ar Najeriya ke shirin yi a kan gazawar shugaban kaa, Bola Tinubu.
An samu asarar rayukan mutum hudu bayan wani gini ya rufto musu a jihar Legas. Hukumomi sun samu nasarar ceto mutum biyar da lamarin ya ritsa da su.
Jihar Legas
Samu kari