Jihar Legas
Masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya sun koka bisa yadda jami'an tsaro su ka kashe wasu daga cikinsu a sassan kasar a lokutan da su ke tattaki.
Hankalin mahukuntan makarantar Liberty da ke Ikota a jihar Legas da masu amfani da shafukan zumunta ya koma kan tsohuwar makamar makarantar, Folake Olaleye.
'Yan Najeriya na ci gaba da tururuwa zuwa kan tituna domin nuna adawarsu kan halin kunci da tsadar rayuwar da aka samu a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Masu shirya zanga-zangar da ake yi a jihar Legas sun sanar da tafiya hutun kwana ɗaya tal domin duba abubuwaɓ da suka faru da ɗaukarmataki na gaba.
Haramtacciyar kungiyar 'yan awaren IPOB ta bukaci gwamnatin Najeriya ta ba ta damar kada kuri'a domin tabbatar da matsayarsu a cikin kasar nan da kansu.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan daba sun farmaki masu zanga-zanga da suka yi dafifi a kusa da ofishin Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas a ranar Litinin.
Wasu daga cikin jagoroin kungiyoyin da ke gudanar da zanga-zanga sun bayyana janyewarsu bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabin neman tattaunawa.
Jagororin matasa sun sanar da janye zanga-zangar da suke yi a yankin Ojota da ke jihar Legas bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da jawabi a safiyar Lahadi.
Wasu matasa sun tarwatsa masu zanga-zanga a yankin Ojota da ke jihar Lagos da cewa ai Shugaba Bola Tinubu ya riga ya yi jawabi ga 'yan kasar kan matsalar.
Jihar Legas
Samu kari