Lafiya Uwar Jiki
Shi dai itace ruman a turance ana kiran sa Pomegranate, kuma ya samo wannan suna ne daga sunan sa larabci wato Rumman, inda Allah madaukakin sarki ya ambace sa a wurare daban-daban a cikin ayoyin sa na Al-Qur'ani mai girma.
Mutane da dama kan yi dariya ne a yayin da suke cikin nishadi ko walwala. Wani abun al'ajabi na dariya shine ba ta da yare ko kabila domin kuwa kowa na yinta, sai dai da yawan masu yin dariya ba su da masaniyar amfaninta.
Bawon ayaba yana kunshe da arziki na sunadaran gina jiki (nutrients) da kuma masu sanya karfin jiki (carbohydrates). Akwai ire-iren sunadaran vitamin B6, vitamin B12, magnesium da kuma Potassium wadanda suke da alfanu daban-daban.
Ga masu neman hanya mafi sauki don inganta rayuwar su da kuma lafiyar su fiye da komai, shan ruwan lemun tsami a farkon kowace safiya abu ne mai sauki da mutum zai rinka yi kuma zai yi tasiri wajen lafiya managarciya.
Hanta da Koda suna bukatar wadataccen ruwa a jikinsu don haka yayin da bawa ya zama yana amfani da ruwa mai sanyi zai zamo su kuma suna cutuwa ta yanda aikinsu zai fara raguwa inda haka ke jefa mutum cikin matsala.
Binciken masana nazari a kan kiwon lafiya ya bayyana amfanin citta a jikin dan Adam. Tun tsawon shekaru sama da 4, 700, mutanen kasar Sin da Indiya ke amfani da citta wajen magance cututtuka daban-daban.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Bashir dalibi ne da ya riki sana'ar nika yayin da yake zaman jiran sakamakon kammala karmar sakandire (junior WAEC) a makarantar gwamnati ta jeka ka dawo da ke unguwar Tudun
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an karrama wata mata a jahar Kaduna wanda ta ciri tuta a tsakanin iyaye mata a jahar ta bangaren kwarewa wajen iya da shayar da jariransu na tsawon lokaci.
Wani mummunan bala'i ya auku a birnin Ikko na jihar Legas yayin da ajali ya katse hanzarin wani mutum yana tsaka da sassarfa a kan hanyar WEMCO da ke yankin Ogba da sanyin safiyar ranar Lahadin da ta gabata.
Lafiya Uwar Jiki
Samu kari