Kyan kai: Atiku Abubakar zai gina kafataren Asibiti a babban birnin tarayya Abuja

Kyan kai: Atiku Abubakar zai gina kafataren Asibiti a babban birnin tarayya Abuja

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya sanar da kammala yarjejeniya da kungiyar Asibitocin Saudi German dake Dubai don gina wani katafaren Asibiti na zamani a babban birnin tarayya Abuja.

Atiku ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 28 ga watan Mayu a yayin taron tattaunawa da yayi da wakilan Asibitocin Saudi Germna a karkashin jagorancin Rajeev Kaushal, inda yace shirya gina Asibitin mai dauke da gadaje guda 100.

KU KARANTA: Yadda aka kusa kashe ni a wata kasuwa a jihar Kaduna – Inji wata tauraruwar Kannywood

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Atiku yana fadin idan aka kammala aikin asibitin, yan Najeriya zasu rage fita kasashen waje da nufin neman magani, haka zalika zai dauki kwararrun likitocin kasashen waje aiki, da zasu horas da likitocin Najeriya.

Kyan kai: Atiku Abubakar zai gina kafataren Asibiti a babban birnin tarayya Abuja
Atiku Abubakar

Shi ma a nasa jawabin, Kaushal yace: “Asibitin da zamu gina tare da kamfanin West Africa Health Care Company Limited na Atiku Abubakar zai samar da dukkanin kayan aikin magance kusan dukkani cututtukan da ake dauka daga mutum zuwa mutum.” Inji shi.

A wani labarin kuma, tsohon shugaban kasa Atiku ya nada tsohon gwamnan jihar Ogun,Otunba Gbenga Daniel a matsyain jagoran yakin neman zabensa a takarar kujerar shugaban kasar Najeriya da ya kuduri tsayawa a shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel