Illolin Koren Shayi ga Lafiyar 'Dan Adam

Illolin Koren Shayi ga Lafiyar 'Dan Adam

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Guardian sun bayyana cewa, a shekarar 2016 da ta gabata ne, a kayi gaggawar garzayawa da wata yarinya zuwa asibiti bayan kwanaki uku da kwankwadar koren shayi a kasar Birtaniya.

Illolin Koren Shayi ga Lafiyar 'Dan Adam
Illolin Koren Shayi ga Lafiyar 'Dan Adam

Binciken kwararrun lafiya ya tabbatar da wannan yarinya ta kamu da cuta da ta yiwa hantar jikin ta mummunan lahani.

Kamar kullum masana sirrin ababen ci da sha su kan bayar da shawarwari akan mashahurin amfani ga kiwon lafiya da ta'ammali da koren shayi ke yiwa jikin dan Adam, kamar irin su rage teba da nauyin jiki, hakan ba ya nuni ga nakasun illolin sa.

Tamkar kowane nau'i na shayi, koren shayi yana kushe da sunadarin Caffeine mai matukar illa ga lafiyar dan Adam duk da dai adadin sa kasa yake da sauran nau'ikan na shayi.

Wannan sunadari na Caffeine da koren shayi ke tattare da shi ya sanya bincike yake gargadin yawaitar ta'ammali da shi akan nau'ikan cututtuka da kuma lahani da ya ka iya janyowa dan Adam.

Kwararrun kiwon lafiya sun bayar da shawar ta takaita kwankwandar kofin shayin sau guda zuwa sau biyar a kowace rana, inda yawaitar amfani da shi ka iya janyo cututtuka da suka hadar da:

1. Ƙwannafi

2. Rashin lafiya ta Jini (Anaemia)

3.Ciwon Sukari

4. Raguwar Sunadarin Iron a jikin dan Adam

5. Nakasun nagartar Kashin dan Adam

6. Hawan Jini

7. Ciwon Ciki

8. Bugun Zuciya

9. Ciwon Idanu (Glaucoma)

KARANTA KUMA: Taron Jam'iyya: Okorocha da shugabannin APC na Jihar Imo sun gana da Osinbajo

Binciken ya tabbatar da cewa daya daga musabbai dake janyo wannan cututtuka shine kwankwadar koren shayi ba tare da sanya abinci a ciki ba, wanda hakan ke janyo barazana ga hantar dan Adam.

Kwararrun kiwon lafiya sun bayar da shawar ta kwankwadar koren shayin sa'o'i biyu gabanin cin abinci, inda kuma suka yi gargadin ta'ammali da shi a lokutan sanyi mai matukar tsanani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng