Yadda Ciwon Zuciya ke kassara Maza yayin da suka kai shekaru 40 a Duniya

Yadda Ciwon Zuciya ke kassara Maza yayin da suka kai shekaru 40 a Duniya

Farfesa Janet Ajuluchukwu, wata kwararriyar likitar Zuciya dake karantarwa a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jihar Legas a yankin Idi-Araba ta bayyana cewa, Maza sun yiwa Mata zarra da Fintinkau wajen kamuwa da matsalolin da suka shafi zuciya.

Farfesa Janet take cewa, adadin maza da ciwon zuciya ke kassarawa a halin yanzu ya ninku biyu yayin da suka haura shekaru 40 a Duniya.

A ranar Asabar din da ta gabata ne Ajuluchukwu ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a jihar Legas.

Farfesan ta bayyana cewa, binciken da aka gudanar ya tabbatar da yadda mafi akasarin maza ke rashin ziyartar asibiti sai bayan wannan cutar ta ciwon zuciya ta ci karfin su da babu wata hanya da za a iya magance ta.

Yadda Ciwon Zuciya ke kassara Maza yayin da suka kai shekaru 40 a Duniya
Yadda Ciwon Zuciya ke kassara Maza yayin da suka kai shekaru 40 a Duniya

Kwararrar Likitar ta jaddada shawarar ta ga maza akan su rika ziyartar asibiti akan kari lokaci bayan lokaci domin matsaloli irin su hawan jini ba sa bayyana wata alama yayin da suka yi lafiyar dan Adam hawan kawara.

KARANTA KUMA: Jami'in 'Dan sanda ya Farauci wani 'Dan Kabu-Kabu har Mutuwar sa kan Cin Hanci Na N100 a Jihar Anmabra

Hasashen Farfesan ya bayyana cewa, mafi akasarin maza su na da ra'ayi da kuma akidar cewa sun dara Mata ta fuskar karfi da hakan yake sanya wa ba su ziyartar asibiti domin Likitoci su duba lafiyar su.

Take cewa, wannan akida ta sanya maza su ke ganin ziyartar Asibiti yayin da cuta ta damke su a matsayin nakasu ko kuma wani rauni a gare su. A wani sa'ilin da har suke bugun gaba da cewar sun shafe wani tsawon lokuta ba tare da

A yayin haka Farfesa ta nemi mata da suka da 'yan uwa maza akan kara karfin gwiwa da shawartar su wajen ziyarar Asibiti domin duban lafiyar su lokaci bayan lokaci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng