Yadda Kindirmo ke Maganin Ciwon Asma da Kumburin Gabbai
Wani sabon bincike ya bayyana yadda sarrafaffen Kindirmo da ake cewa Yogurt a Turance yake taka muhimmiyar rawar gani wajen dakile kwayoyin cututtuka dake haddasa ciwon Asma da kumburin gabbai na jikin dan Adam.
Wannan sabon bincike da aka wallafa a mujallar Journal of Nutrition ya bayyana yadda kumburin jiki ke da matukar tasiri wajen bayar da garkuwa ta cututtuka a jikin dan Adam.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, kumburin jiki yana da alaka da garkuwar jiki ta kawo nakasun lafiyar wasu muhimman sassa a jikin dan Adam da suka hadar har da cututtukan zuciya.
An gudanar da wannan sabon bincike ne a jami'ar Wisconson-Madison dake kasar Amurka, inda ya bayyana cewa Yogurt yana hana kumburin jiki wanda a sanadiyar hakan yake inganta lafiyar hanji tare da bayar da garkuwar cututtuka ga jinin jiki.
KARANTA KUMA: Ministan Lafiya ya bayyana dalilin da ya sanya Shugaba Buhari ke neman Lafiyar sa a Kasashen Turai
Jagoran wannan bincike, Dakta Brad Bolling ya kara da cewa, bincike da suka gudanar ya tabbatar da Yogurt na daya daga cikin nau'ikan abinci masu hana kumburin jiki da gabbai da hakan yake taimakawa wajen dakile cutar Asma da masu dangantaka da ita.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng