Rashin kudi ne ya sanya ni halin dana ke ciki a yanzu
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta jihar Edo ta kama wani mai suna Raymond Ojero, mai shekaru 40, da Indian Hemp mai nauyin kilo 37, wadda kudin ta ya kai kimanin naira 370,000
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta jihar Edo ta kama wani mai suna Raymond Ojero, mai shekaru 40, da Indian Hemp mai nauyin kilo 37, wadda kudin ta ya kai kimanin naira 370,000.
DUBA WANNAN: Ashe har FIFA ta riga ta biya 'yan kwallon Najeriya kudaden su tun kafin a fara buga gasar kofin duniyan
Mun samu rahoton cewa an kama mai laifin da kulli - kulli na tabar wiwi har guda 47 daure a cikin jakankuna, a cikin motar haya akan babbar hanyar Auchi.
Da yake magana da manema labarai, wanda ake zargin ya amsa laifin sa, inda ya bayyana cewar ya shiga harkar sayar da miyagun kwayoyin ne dalilin ya samu matsala a kasuwancin da yake yi na sayar da shanaye.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng