Wasu jami'o'i uku a Najeriya za su fara digiri a fanin nazarin magungunan gargajiya
- Jami'o'in Najeriya gudu uku za su fara bayar da horo a kan ilimin magungunan gargajiya ta Najeriya da Afirka
- Jami'o'in sun hada da Jami'ar Ilorin, Jami'ar Samuel Adegboyega a jihar Edo da kuma Jami'ar nazarin kimiyyar lafiya ta Ondo
- An bullo da shirin ne don taimakawa masu magungunan gargajiya samun kwarewa a sana'arsu
Babban direktan wata kamfanin bincike da sarrafa magunguna ta Pax Herbal Clinic and Research Laboratories, Rev. Anselm Adodo ya ce kamfaninsa ta sa hannu a wata yarjejeniya da wasu jami'o'i uku a Najeriya don fara gabatar da karatun digiri da Certificate a fanin nazarin magungunan gargajiya.
A lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a yau Laraba, Adodo ya ce Jami'ar nazarin kimiyyar lafiya ta Ondo tana shirye-shiryen fara gabatar da ilimin digiri a fannin magungunan gargajiyar.
KU KARANTA: 2019: Tsaffin 'yan PDP da suka dawo APC ba za su iya kawo wa Buhari cikas ba - Ganduje
"Wannan wata babban mataki ne wajen habbaka ilimi da bincike a kan magungunan gargajiya a Najeriya," inji shi.
Ya kuma ce a halin yanzu Jami'ar Samuel Adegboyega da ke garin Ogwa a jihar Edo tana gab da fara bayar da shedar Certificate a fanin ilimin magungunan gargajiyar, tuni Jami'ar Ilorin ta amince da fara digiri na biyu MSc da digiri ta uku PhD a fanin binciken magungunan gargajiya na Afrika.
"An kuma gabatar da darasi a kan magungunan gargajiya a sashin binciken kimiyyar sarrafa magunguna a jami'ar Ibadan," inji shi.
Adodo ya kuma bayyana cewa Pax Herbal ta fara hadin gwiwa da sashin binciken magungunan gargajiya na Afirka don fara bayar da horo ta Certificate a fanin magungunan gargajiyar.
An bullo da shirin ne don karfafa gwiwar masu magungunan gargajiya da muke da su don su samu kwarewa a sana'arsu, inji Adodo.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng