Ana haihuwar Yara 150, 000 da cutar Amosanin Jini a kowace shekara - Babadoko
Wani kwararren Likitan jini dake asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello, Farfesa Aliyu Babadoko a ranar talatar da ta gabata ya bayyana cewa ana haihuwar yara 150, 000 masu dauke da cutar amosanin jini watau ciwon Sikila cikin kowace shekara a fadin Najeriya.
Babadoko ya bayyana hakan ne yayin gabatar da wata lacca a jami'ar jihar Kaduna yayin tunawa da ranar Cutar Sikila ta Duniya.
Kwararren likitan ya bayyana yadda cutar amosanin jini ta zamto ruwan dare mai game duniya a halin yanzu.
Yake cewa, akwai kimanin mutane Miliyan 20 zuwa 25 masu dauke da cutar amosanin jini a duniya yayin da kimanin Miliyan 12 zuwa 15 sun kasance mazauna yankin Afirka inda ake haihuwar yara 300, 000 dauke da cutar cikin kowace shekara a fadin Duniya.
Legit.ng ta fahimci cewa, cikin wannan kaso kasar Najeriya na haihuwar yara 150, 000 masu dauke da cutar amosanin jini inda take dauke kaso 2 zuwa 3 cikin 100 na adadin masu cutar a Duniya.
Wani bincike kamar yadda babban Likitan ya bayyana, kasashen Najeriya, India da kuma Jamhuriyyar Congo na bayar da kaso 90 cikin 100 na adadin masu cutar amosanin Jini a fadin Duniya.
Ya kara da cewa, nahiyyar Afirka ta ciri tuta ta mafi adadin masu dauke da cutar amosanin Jini a duniya hakazalika ita nahiyya kan gaba wajen cutar zazzabin cizon sauro.
KARANTA KUMA: Tabbas: Shugaba Buhari zai sanya Hannu ga Kasafin Kudin 2018 a gobe Laraba - Fadar Shugaban Kasa
A nasa jawaban, shugaban jami'ar ta Kaduna, Farfesa Muhammad Tanko ya bayyana cewa, ana fama da wannan barazana a kasar nan ne sakamakon watsi da ilimi da kalubalai na cutar amosanin jini cikin shekarun da suka shude.
Farfesa Tanko ya kuma bayyana damuwar sa dangane da yadda mutane musamman a Najeriya ke rufe idanun su cikin shauki na soyayya ba tare da sanin irin nau'in jini dake gudana cikin jikin su kafin su auri juna, wanda mafi akasarin haka ke sanadiyar haihuwar yara masu cutar Sikila.
A sanadiyar haka shugaban jami'ar ya nemi a kara kaimi a kasar nan wajen wayar da kawunan al'umma tare da fadakar da su dangane da ilimi da kuma kalubalai tare da hanyoyi na kiyaye yaduwar cutar a kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng