Kasar Saliyo ne bidar likitoci da malaman makaranata daga Najeriya

Kasar Saliyo ne bidar likitoci da malaman makaranata daga Najeriya

Ministan harkokin kasashen waje na kasar Saliyo, Allie Kabba ya nemi tallafi daga Najeriya a fannin ilimi, kiwon lafiya da makamashi. Mr. Kabba ya yi wannan rokon ne a ranar Laraba a Abuja yayin da ya ziyarci takwaransa na Najeriya, Geoffrey Onyeama a ofishinsa.

Ya ce al'ummar Saliyo sun zabi wannan sabuwar gwamnatin ne saboda alkawurran da ta dauka musu kuma gwamnatin a shirye ta ke don gannin da cika wadannan alkawurran da kuma samar da ingantaccen shugabanci.

Ya yi bayyani cewa samar da ingantaccen ilimi shine abu na farko cikin tsare-tsaren gwamnatin kuma gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen cika wadannan alkawurran.

Kasar Saliyo ne bidar likitoci da malaman makaranata daga Najeriya
Kasar Saliyo ne bidar likitoci da malaman makaranata daga Najeriya

KU KARANTA: Sharudda hudu da 'yan nPDP suka gindayawa jam'iyyar APC

Mr. Kabba ya ce, "Ina fatan Najeriya za ta taimaka mana wajen samar da ajujuwan karatu har ma da malamai kwararu.

"Yarjejeniyar hadin gwiwa da mu kayi shekaru da suka gabata ya nuna cewa za'a aike da kwararun malamai daga Najeriya domin su taimaka mana."

A cewarsa, irin wannan taimakon zai taimaka sosai wajen ganin cewa gwamnatin da cinma burinta na cika alkawurran da ta dauka wa mutanen kasar.

Ya kuma kara da cewa kasar tana daukan fanin kiwon lafiya da muhimmanci hakan yasa kasar ke kokarin farfado da fanin kiwon lafiyan tun bayan yakin basasa da akayi a kasar.

"Muna fama da karancin kayayakin bincike na lafiya hakan yasa masu hannu da shuni a kasar ke zuwa Ghana ko Najeriya don duba lafiyarsu.

"Kuma hakan yakan sa kasar rasa kudaden shiga sosai din haka zaiyi kyau a ce kasar ta mallaki na ta kayan binciken." inji shi.

Ministan ya mika godiyarsa ga likitoci da ma'aikatan jinyar Najeriya da ke taimakawa a kasar tare da fatan za'a cigaba da taimaka musu.

A bangarensa, Onyeama ya yi alkawarin cewa Najeriya za ta cigaba da taimakawa kasar ta Saliyo a karkashin shirin Technical Aid Corps tunda kasashen biyu dama suna da yarjejeniyar taimakawa juna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel