Ko ka san illolin da shisha ke yiwa jikin dan adam?
Shan shisha ya zama ruwan daren a Najeriya kuma ba'a masa kallon wani abu mai hadari misali tsakanin matasa a cewar shugaban sashin kula da cuttuka masu yaduwa na ma'aikatar lafiya na tarayya, Dacta Nnnena Ezeigwe.
Ta ce abin damuwa ne yadda shan shishia ke kara bazuwa a birane, ta koma koka kan yadda ake sayar da shishan a sawakke a shaguna har ma da yanan gizo.
"Matasa da dama da ke busa hayakin shisha a suna tunanin ba ta da wani hadari ga rayuwarsu, wasu kuma na tunanin cewa ba ta kai tabbar sigari hadari ba sai dai ba haka zancen ya ke domin illar shisha ta rubanya na cigabar nesa ba kusa ba," inji ta.
KU KARANTA: A karo na farko, mahaifiyar Shekau tayi magana a kan Boko Haram
Ta ce galibi idan an zauna shan shisha a kan dauki tsawon sa'a guda kamar yadda wasu binciken da akayi suka nuna, akwai yiwuwar za'a shaki hayakin da ya kai misalin cigari 100.
Sai mai masu binciken lafiya da kwararun likitoci sunyi gargadin cewa shima shisha yana yiwa lafiyar dan adam illa sosai har ma fiye da tabbar cigari kana mutum na iya zama ya dogara ga shan ta har ma idan bai sha ba zai shiga wani hali.
Dr. Ezeigwe tace shisha yana da kamanceceniya da cigari domin yana dauke da sinadarin nicotine wanda shine abinda ya ke kan gaba wajen haifar da cutar Cancer a cikin tabar cigari.
Baya ga haifar da cutar Cancer, Dr. Ezeigwe ta ce nicotine ya saukaka wa mutum kamwa da wasu cututuka kamar ciwon huhu, ciwon suga, matsalar numfashi da kuma asthma. Ta kuma ce yana janyo rashin haihuwa ga maza, haihuwan bakwaini ga mata da ciwon ulcer da kuma hauka.
Kazalika, mutum na iya daukan ciwon tarin TB ko hepatitis ta hanyar zukar shishan bayan wani mai cutar ya sanya bakinsa ya zuka ya mika maka.
Likitan ta shawarci masu shan shishar da suyi kokari su dena duk da cewa idan aka saba akwai wutar denawa. Ta ce akwai hanyoyin da likitoci za su iya taimakawa mutane masu son dena shan shisha ko tabar cigari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng