WHO ta samar da wani sabon magani da zai ke taimakawa wurin ceto mata masu mutuwa a wurin haihuwa
Hukummar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta ce ta samo wani sabon magani mai suna Carbetocin wanda zai iya ceto dubunnan matan da ke rasa rayukansu gurin haihuwa a duk shekara
Hukummar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta ce ta samo wani sabon magani mai suna Carbetocin wanda zai iya ceto dubunnan matan da ke rasa rayukansu gurin haihuwa a duk shekara.
Kungiyar tace an inganta maganin da sababbin fa'idoji fiye da sinadarin Oxytocin wanda ake amfani dashi gurin tsayar da zubar jini bayan haihuwa.
DUBA WANNAN: Dalilin da yasa kabilar Himba basa yin wanka
WHO tace zubar jinin da ya wuce misali bayan haihuwa yana kashe kusan mata 70,000 a duk shekara, inda sinadarin Oxytocin ake amfani da gurin magance matsalar.
Binciken wanda wani bangaren WHO suka jagoranta, sun fitar da sakamakon a ranar laraba. Sunce sabon maganin da za a iya adana shi a matsakaicin yanayi, zai iya tseratar da rayukan dubunnan mutane a kasashe masu karami da matsakaicin karfi.
"Wannan gaskiya zai karfafa sababbin cigaban da zai iya tseratar da rayukan iyaye mata da jariran" inji darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
WHO tace dole a adana sinadarin Oxytocin daga degrees 2 zuwa degrees 8,wannan ya zama barazana ga mataye da dama, inda basa samun maganin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng