Lafiya uwar jiki: Sabubba guda 6 dake janyo ciwon baya ga jikin dan Adam

Lafiya uwar jiki: Sabubba guda 6 dake janyo ciwon baya ga jikin dan Adam

Guda cikin cuiwuka da suke yawan damun jama’a shi ne ciwon baya, kamar yadda likitoci suka tabbatar. Shi dai ciwon baya wani ciwo ne da ya kunshi tsokokin, jijiyoyi, lakka, da kasusuwan da suke bayan mutum, wanda aka fi jinsa a tsakiyar baya, daga kasar hakarkari zuwa kugu.

Likitoci sun tabbatar da cewar yana ciwon ya kanzo a kamar wani tsunguli, ko kuma wani ciwo da ba zai misaltu ba saboda zafin da yake da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito, don haka muka kawo muku sabubban dake sabbaba ciwon baya, dasuka hada da:

KU KARANTA: Hare haren Yan bindiga: Sanata Shehu Sani ya zargi El-Rufai da daukan nauyin yan bindiga a Jihar

1- Rikewar tsokoki da jijiyoyi

2- Rashin isashshen motsa jiki

3- Cinyewar mahada

4- Raunin tsokokin baya

5- Yin ayyuka ba a daidai ba

6- Buguwa sakamakon hatsari ko faduwa

Lafiya uwar jiki: Sabubba guda 6 dake janyo ciwon baya ga jikin dan Adam

Ciwon baya

Akwai wasu cututtuka na daban wadanda suma suna yin dalilin kamuwa da ciwon baya, ire iren cututtukan nan sun hada da Ciwon Daji, sanyin kasha, tarin fuka, yawan shekaru, yawan aiki a tsaye, daukan kaya masu nauyi, yanayin wajen kwanciya, kiba, al’ada da sauransu.

Hakazalika, wasu daga cikin alamomin ciwon baya sun kunshi:

1- Rikewar idan an tashi daga barci

2- Saukar ciwon zuwa kafafuwa

3- Saurin gajiya

4- Kagewar baya yayin aiki

Babbar hanyar magance wannan ciwo da ta zama gama gari shi ne ta hanyar tafiya Asibiti don samun kwaarrren likitan kasha ya duba mara lafiya, sai dai akwai wasu hanyoyi da akan iya binsu kamar:

1- Shan kwayoyi masu rage radadin ciwo

2- Shan magungunan gargajiya

3- Yin kaho don cire gurbataccen jinni a jiki

4- Samun isashshen hutu

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel