Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

Babu shakka shan ruwan sanyi yana da matukar dadi da musamman ma lokacin da gari ya yi zafi, sai dai duk dadinsa, masanna sun gano cewa akwai wasu illoli da ya ke haifar wa a jikin dan adam saboda haka ya zama dole a rika takatsantsan idan har ana son kaucewa wannan matsalolin.

1. Rage karfin bugun zuciya: Bincike ya nuna cewa shan ruwa mai sanyi sosai yana rage karfin bugun zuciya har ma wani lokaci da kai ga tsayawa wanda hakan kuma ya iya zuwa da karen kwana.

Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam
Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

2. Rashin narkar da abinci kan lokaci: Ruwan sanyi da sauran ababen sha masu sanyi suna kawo cikas wajen narkewar abinci a cikin dan adam. Hakan na faruwa ne saboda jikin mutum na aiki sosai wajen dumama ruwan ya yi dai-dai da yanayin zafin jikin mutum kafin abincin ya fara narkewa da kyau.

Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam
Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

3. Tauye karfin jiki: Masana sunyi gargadi game da shan ruwan sanyi musamman bayan an gama motsa jiki duk da cewa mutane da dama na aikata hakan. Masana harkokin motsa jiki suna sharwartar mutane su sha ruwa mara sanyi bayan kammala motsa jikin domin na'urorin jikin mutum na wahala sosai wajen dumama ruwan don zama dai dai da jiki. Kazalika, hakan na iya janyo ciwon ciki.

Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam
Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

4. Karin kiba: Shan ruwan sanyi musamman bayan an ci abinci yakan kawo wa jiki cikas wajen narkar da abincin musamman nau'in abinci mai maiko domin ruwan sanyi yana daskarar da maiko kuma yakanyi wahalar narkewa ya bi jiki. Rashin narkewar maikon da wuri kuma na iya janyo tsukewar hanyoyin jini.

5. Wahalar fitar ba haya: Duk da cewa shan ruwa yana da muhimmanci wajen narkar da abinci sai dai shan mai sanyi karara ya kan haifar da akasin hakan. Dalili kuwa shine ruwan sanyin na daskarar da abinci musamman ma idan abincin mai maiko ne. Hakan kuma ke sanya mutum ya rika shan wahala wajen fitar bayan gida.

Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam
Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164