Labarin Sojojin Najeriya
Rikici ya barke tsakanin ’yan sanda da sojojin sama a Delta kan sakin wanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi. Ana binciken lamarin don shawo kan matsalar.
Sojoji sun fatattaki 'yan fashi da makami da suka tare hanyoyi a jihar Kaduna suna kokarin sace mutane. 'Yan fashin sun firgita sun tsere, an ceto mutane biyu.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da zaman lafiya sun samu nasarori kan 'yan ta'adda a jihohin Zamfara da Sokoto. Sojojin sun hallaka kwamandoji masu yawa.
Dubun wani baragurbin likita mai kula da lafiyar 'yan ta'adda ta cika a jihar Katsina. Likitan ya amsa zargin da ake masa inda ya yi bayani kan ayyukansa.
Dakarun rundunar sojin Najeriya a jihar Filato sun harbe wani dan bindiga mai suna Hamisu Saleh da ya yi kokarin kwace bindiga a hannun soja. An harbe shi har lahira
Al’ummar Kuryar Madaro da ke Zamfara sun koka kan sabon sansanin ɗan ta'adda, Dan Sa’adi da ke kai hare-hare. Sun nemi karin matakan tsaro daga gwamnati.
Wasu shahararrun 'yan bindiga sun tuba daga aikata ayyukan ta'addanci a jihar Katsina. 'Yan bindigan sun mika wuya tare da ba jami'an tsaro makamansu.
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya bayyana cewa domin magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita, sojojin Najeriya na bukatar fiye da makamai.
Rundunar sojin Najeriya ta cafke wani fitaccen mai safarar makamai ga 'yan bindiga a jihar Zamfara yayin da yake kokarin guduwa a lokacin da aka cimmasa.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari