Sojojin Sama Sun Kai Farmaki Sansanin 'Yan Ta'adda, Sun Sheke Miyagu Masu Yawa

Sojojin Sama Sun Kai Farmaki Sansanin 'Yan Ta'adda, Sun Sheke Miyagu Masu Yawa

  • Rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana cewa ta samu nasarar lalata wani sansanin ƴan ta'adda a jihar Kaduna
  • Mataimakin daraktan yaɗa labarai na rundunar ya bayyana cewa sansanin na wani shugaban ƴan ta'adda mai suna Kadade Gurgu
  • Kyaftin Kabiru Ali ya bayyana cewa farmakin da aka kai ya yi sanadiyyar lalata sansanin tare da hallaka ƴan ta'adda masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Jirgin yaƙin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ya kai farmaki kan sansanin ƴan ta'adda a jihar Kaduna.

Jirgin yaƙin na rundunar Operation Whirl Punch (OPWP) ya lalata sansanin ƴan ta'adda da ke dajin Yadi a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram

Sojoji sun lalata sansanin 'yan ta'adda a Kaduna
Sojojin sama sun lalata sansanin 'yan ta'adda a Kaduna Hoto: Sodiq Adelakun
Asali: Getty Images

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na NAF, Kyaftin Kabiru Ali ya fitar, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka lalata sansanin

Sanarwar ta ce an kai harin ne a ranar Juma’a, 27 ga watan Satumba, 2024, biyo bayan wasu sahihan rahotannin sirri da suka nuna akwai ɗimbin ƴan ta’adda da makamansu a dajin Yadi.

Ya ce bayanan sirrin sun tabbatar da kasancewar ƴan ta’adda da baburansu a wurin, rahoton da jaridar The Nation ta tabbatar.

Sanarwar ta ce, ƙarin bayanan da aka samu sun nuna cewa sansanin kayan aikin mallakar fitaccen shugaban ƴan ta'addan ne, Kadade Gurgu, wanda na hannun daman Dogo Gide ne.

"Wasu bayanan sirri da ke hannun NAF sun nuna cewa Kadage Gurgu yana ba da mafaka ga shugabannin ƴan ta’addan da suka tsero daga Sokoto da Zamfara saboda ruwan wutan da sojoji ke yi musu."

Kara karanta wannan

Bello Turji: Sheikh Pantami ya fadi dalilin ƙaruwar ta'addanci duk da rajistar NIN

- Kyaftin Kabiru Ali

An sheƙe ƴan ta'adda masu yawa

Kyaftin Kabiru Ali ya ƙara da cewa bayan samun bayanan an tura jirgin sama wanda ya kai hari a sansanin.

A cewarsa, rahotanni daga wasu masu ba da bayanai a yankin, sun tabbatar da cewa an lalata sansanin kayan aikin gaba ɗaya tare da kashe ƴan ta’adda da dama a sakamakon harin.

Sojoji sun murƙushe ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar MNJTF na Operation Hadin Kai sun daƙile wani yunƙurin kai hari da ƴan ta'addan Boko Haram suka yi a Borno.

Dakarun sojojin sun yi wa ƴan ta'addan kwanton ɓauna inda suka murƙushe su kafin su kai wa fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba hari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng