Labarin Sojojin Najeriya
Dakarun sojojin Najeriya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a juhar Katsina, sun samu nasarar kubutar da wasu tarin mutane da 'yan ta'adda suka ƴi garkuwa da su.
Mutane sun shiga tashin hankali a jihar Nasarawa bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe jami'an soji uku da 'yan banga biyu a kauyen Umaisha, karamar hukumar Toto.
Majalisar dattijan Najeriya ta canza tunani bayan manyam hafsoshin tsaron ƙasa sun bayyana a gabanta, ta umarci su tafi su sake dawowa ranar Talata a mako mai zuwa.
Majalisar dattawa ta shirya ganawa da hafsoshin tsaron kasar nan kan matsalar rashin tsaro da ake ci gaba da fama da ita a sassa daban-daban na kasar nan.
Hukumomin tsaro sun fito sun yi magana kan zargin da ake yo wa wani sanatan Arewa na daukar nauyin ta'addanci. Hukumomin sun ce zargi ne mara tushe.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar fatattakar 'yan bindiga daga maboyarsu a jihar Taraba. Sojojin sun kuma kubutar da mutanen da aka sace.
Mayakan Boko Haram sun kashe mutum biyu a a wata cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Kuareta, kilo mita 20 nesa da garin Damaturu. Gwamnati ta tabbatar da harin.
Dakarun sojoji sun samu nasarar sheje 'yan ta'adda masu tarin yawa a wani samame da suka kai a maboyarsu da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
A ranar Asabar ne sojoji suka kama wasu mutane biyu ciki har da shugaban matasa a karamar hukumar Afikpo yayin zaben maye gurbin Sanatan Ebonyi ta Kudu.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari