DHQ: Dalilin Bada Umarni ga Duk Wani Tsohon Janar Ya Yi Ritaya Cikin Awanni 72

DHQ: Dalilin Bada Umarni ga Duk Wani Tsohon Janar Ya Yi Ritaya Cikin Awanni 72

  • Sanarwa ta fito daga DHQ cewa duk sojan da yake gaban sababbin Hafoshin tsaro ya ajiye aikinsa
  • Hedikwatar tsaro za tayi wa manyan jami’anta ritaya kamar yadda aka saba idan an canza shugabanni
  • Manjo Janar Y. Yahaya ya sa hannu a takardar da aka fitar mai lamba DHQ/I5/PLANS/801/13

Abuja - Hedikwatar tsaro ta bada umarni ga duk sojan da ke gaban sababbin hafsun sojojin da aka nada, ya yi murabus ba tare da wani bata lokaci ba.

Hedikwatar da ke babban birnin tarayya na Abuja ta bada wa’adi zuwa Litinin domin manyan sojojin su yi ritaya da kan su, rahoton nan ya fito a Punch.

Manjo Janar Y. Yahaya ya fitar da wannan sanarwa a madadin shugaban hafun tsaro na kasa. Takardar ta fito ne tun a ranar Litinin, 26 ga Yuni 2023.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Jam'iyyar PDP Ta Yabi Tinubu Kan Matakan Da Ya Ke Dauka, Ta Ce Ya Yi Bajinta

Sojoji
Wasu sojoji a bakin fama Hoto: DefenceInfoNG
Asali: Facebook

Su wanene abin ya shafa?

Wadanda umarnin ya shafa sun hada da wadanda su ka kai matsayin Janar, Manjo Janar, Air Vice Marshal da Rear admiral na sojojin kasa, ruwa da sama.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Takardar mai lamba DHQ/I5/PLANS/801/13 ta wajabtawa duk wanda ya ke gaba da ‘yan aji na 39 a makarantar sojoji ta NDA, ya rubuta takardar ritaya.

An dauki wannan mataki ne domin tabbatar da ladabi da biyayya kamar yadda aka saba.

Sojoji nawa za su bar aiki?

Da aka tuntubi Onyema Nwachukwu domin jin adadin sojojin kasan da abin zai shafa, jaridar ta rahoto kakakinsu ya na cewa ba zai iya sanin yawansu ba.

Shi ma dai Adedotun Ayo-Vaughan ya nuna a halin yanzu ba zai iya fadin yawan sojojin ruwa da za ayi wa ritaya a sakamakon nadin sababbin hafoshin ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

Mai magana da yawun sojojin sama, Air Commodore Ayodele Famuyiwa ya ki cewa uffan kan lamarin, yayin da aka gagara tuntubar Janar Gen Tukur Gusau.

An taba Sojojin sama 56

Rahoton Premium Times ya ce a yanzu an canza sojoji 56 wuraren aiki. Wadanda sauyin ya shafa su na kan matsayin Rear Admirals ne da Air Commodore.

Ayo-Vaughan ya shaidawa manema labarai cewa an canza manyan Darektoci da shugabannin da ke Hedikwata da wasu kwamandojin yakin da ke kasar.

Babu maganar binciken Buhari

Duk abin da zai faru, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bada tabbacin ba za ta binciki Muhammadu Buhari wanda ya mika mata ragamar mulki ba.

Rahoton da mu ka samu ya nuna Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya bada wannan tabbaci da kan shi, sai dai tuni Garba Shehu ya musanya wannan batu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel