Labaran Duniya
Kungiyar Raya Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) karkashin jagorancin Tinubu ta fara taronta na musamman kan rikicin siyasa da ya kunno kai a jamhuriyar Nijar.
Tsohon madugun ‘yan tawayen Neja Delta a Najeriya, Asari Dokubo, ya bayyana cewa zai iya lallasa shugabannin sojojin Jamhuriyar Nijar idan har aka ba shi dama.
Ɗan takarar shugaban ƙasar Ecuador, Fernando Villavicencio, ya gamu da ajalinsa bayan an buɗe masa wuta a wajen wani gangamin taron yaƙin neman zaɓe a ƙasar.
Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi ya ce ya yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayani kan ziyarar shiga tsakani da ya kai wa shugabannin sojojin Nijar.
Wani tsohon shugaban yan tawaye kuma dan siyasa a Nijar ya ce ya kafa wata kungiya a kokarin dawo da hambararren Shugaban kasa Mohamed Bazoum kan karagar mulki.
Ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ta sake sanya sabbin takunkumi kan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Bazoum a Jamhuriyar Nijar
Shugabannin ƙungiyar ECOWAS sun gana bayan cikar wa'adin da suka ba Janar Abdourahamane Tchiani ya tattara kayansa ya sauka daga kan madafun ikon ƙasar Nijar.
Gwamnatin sojoji da Janar Abdourahamane yake jagoranta a Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarnin kulle sararin samaniyar kasar bisa tsoron mamayar da za a kawo.
Reno Omokri ya yi magana kan buƙatar Najeriya ta sake dawo da doka da oda a Jamhuriyar saboda ƴan gudun hijira da baƙin haure da za su kwararo zuwa Najeriya.
Labaran Duniya
Samu kari