Labaran Duniya
Dakarun rundunar sojin Isra'ila sun yi ikirarin kakkaɓo jirage marasa matuƙa da ke ɗauke da bam waɗanda Iran ta yi nufin farmar kasar jiya da daddare.
Yayin da ake ci gaba da yaki da Isra'ila, jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya zaɓi malamai uku da za su gaje shi idan aka kashe shi.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa shugaban Iran ya kira shi a waya, kuma sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi shirin nukiliya.
Yayin da ake cigaba da kai hare-hare tsakanin Iran da Isra'ila, tsohon Shugaban Amurka, Bill Clinton ya tona asirin shirin Fira Minista, Benjamin Netanyahu.
Rahoton wata kungiyar kare hakƙin ɗan adama a ƙasar Amurka ya nuna cewa akalla Iraniyawa 65 sun mutu a hare-haren bama baman Isra'ia a mako guda.
Rahotanni daga Iran sun tabbatar da cewa an sanu girgizar ƙasa mai karfin ma'aunin 5.5 Magnitude bayan sallar Juma'a, lamarin ya ƙara rikita ƙasar.
Gwamnatin kasar Iran ta fito ta ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa an hallaka tsohon shugaban kasar, Mahmoud Ahmadinejad a wani hari a birnin Tehran.
Yayin da ake cigaba da faɗa tsakanin Iran da Isra'ila, wata mata mai shekara 51 ta rasu sakamakon bugun zuciya yayin da take buya daga harin makami a Karmiel.
Jamhuriyar musulunci ta Iran ta sake kai farmaki yankunan Isra'ila ranar Juma'a, hukumar agaji ta tabbatar da cewa akalla mutane 17 ne suka raunata.
Labaran Duniya
Samu kari