Labaran Duniya
Rahotanni sun nuna cewa makamai 2 da ake kyautata zaton Iran ce ta harbo su sun faɗa wasu yankuna a ƙasar Jordan, sun raunata yarinya tare da ɓarnata dukiya.
Sanata Ben Murray-Bruce ya ce ya hango cewa ana daf da shiga yakin duniya na uku sakamakon mallakar makamin nukiliya. Ya ce Najeriya za ta zauna lafiya a yakin.
Isra’ila ta tura jiragen yaki, inda suka lalata cibiyar Arak da take zargin Iran na amfani da ita don hada nukiya. Iran ta ce harin bai yi wani barna a cibiyar ba.
Ana hasashen shugaban kasar Amurka, Donald Trump na Amurka zai yanke hukunci cikin makonni biyu ko kasar za ta shiga yakin Isra'ila da Iran da ake yi.
Dakarun rundunar sojin juyin juya hali na Iran sun sanar da kaddamar da hare-hare zagaye na 15 kan manyan biranen Isra'ila, sun ce za su farmaki wuraren soji.
Gwamnatin kasar Ukraine na tsoron cewa rikicin Iran da Isra’ila zai dauke hankalin duniya daga yaki da Rasha, kuma hakan zai karfafa Moscow karfi.
Isra'ila ta yi barazana ga ran jagoran juyin juya hali na Iran, Ayatollah Ali Khamenei. Ministan tsaron Isra'ila ya bayyana cewa bai kamata Khamenei ya rayu ba.
Yayin da ake ci gaba da rigima tsakanin Iran da Isra'ila, an ruguza wani asibiti a birnin a Beersheba bayan harba makami da Iran ta masu linzami.
Rasha ta yi tir da yunkurin da Donald Trump ke yi na shiga yakin Iran da Isra'ila. Shugaban China ya ce tattaunawa da sulhu ne mafita. Putin ne neman yin sulhu.
Labaran Duniya
Samu kari