Kwara
Mai martaba sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya gayyaci manyan malamai an yi taron addu'a ga shugaban ƙasa Tinubu, gwamnan Kwara da Najeriya.
'Yan sanda sun karyata cewa jirginsu ya kai wa 'yan bindiga kaya a Kogi. Sun ce aikin tsaro ne suka gudanar tare da 'yan banga da wasu jami'an tsaro a jihar.
Mummunar gobara ta tashi a kasuwar wayoyi ta Ilorin. An ce wutar lantarki ce ta haddasa gobarar. An dakile wutar cikin lokaci amma rumfuna 10 sun kone.
Hukumar kula da Alhazai ta Kwara ta ce za a fara jigilar farko ta alhazan a ranar 12 ga Mayu, yayin da ta ce an tanadi masauki da abinci har zuwa karshen Hajji.
Shugaban sojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya ba sojojin Najeriya wa'adin wata daya domin murkushe 'yan ta'addan Mahmuda da suka bulla a Arewa.
Sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ta bulla a Arewa mai suna Mahmuda ta fara zafafa hare hare kan al'umma a Kwara. Sun fara kashe mutane a wurare daban daban.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kwara. 'Yambindigan sun bude wuta kan mutane wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayuka.
Jami'an tsaro sun musanta rahoton da ke yawo cewa sabuwar kungiyar ta'addanci mai suna Mahmouda ta ɓulla a Kwara, sun ce wani kwamanda ne a Boko Haram.
Wata kungiyar ta'addanc da ake kira Mahmuda ta bulla a Arewa ta Tsakiya. 'Yan ta'addan sun fara kai hare hare da sanya haraji a yankunan Kwara da Neja.
Kwara
Samu kari