Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Gombe za ta sanya almajirai a tsarin tallafin kiwon lafiya na GoHealth domin ba su kulawa. Dakta Abubakar Musa ne ya sanar da haka a jiya.
Gwamnatin jihar Kano ta gargadi mazauna jihar su yi ta'ammali da ruwan sama bayan an tsaftace shi saboda gudun bullar annobar amai da gudawa a Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci al'ummar jihar da su guji yin amfani da ruwan sama wanda ba a tsaftace shi sakamakon barkewar cutar kwalara a Najeriya.
Gwamnatin jihar Lagos ta tabbatar da mutuwar mutane 24 da kwantar da wasu 34 a jihar bayan sun kamu da cutar kwalara saboda kwankwaɗar kunun aya.
Gwamnan jihar Zamfara, ya kaddamar da aikin gyaran asibitin kwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura da ke birnin Gusau a jihar. Za a daga darajar asibitin.
An samu bullar cutar kwalara a jihar Legas inda ta kashe mutane sama da 21 sannan ta kwantar da mutane sama da 400. Gwamnati ta ce suna kokarin shawo lamarin.
Sama da musulmi 900 ne su ka kwanta dama yayin aikin hajjin bana, yayin da mutane da yawa ke neman ‘yan uwansu da aka nema aka rasa a kasa mai tsarki.
Dubunnan mata suna mutuwa a duk shekara musamman bayan samun juna biyu ko haihuwa. Dr. Zainab Mahmud likita ce a Amurka da ke da burin kawo gyara a Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya yi kira na musamman ga likitoci masu son tafiya kasashen ketare neman aiki kan su zauna a Najeriya.
Kiwon Lafiya
Samu kari