Kiwon Lafiya
Hukumar NAHCON ta bukaci maniyyatan Najeriya da suka isa Makkah da su nemi taimakon likitoci daga duk wani asibitin gwamnatin Saudiyya idan bukatar hakan ta taso.
Gwamnatin tarayya ta yi albishir ga likitocin Najeriya, inda ta ce za ta kara musu albashi nan ba da dadewa ba. Ministan lafiya, Farfesa Ali Pate ya bayyana hakan.
Yayin da duniya ke bikin ranar yara ta duniya, akasarin yara a Najeriya ba za su iya bikin wannan rana ba duba da kangin rayuwa da suke ciki a yanzu.
Ma’aikatar albarkatun noma da wadata kasa da abinci ta gargadi ‘yan Najeriya kan bullar wata cuta a jikin dabbobi a kasuwar dabbobi ta jihar Kwara.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce akalla jarirai 700 ne ke mutuwa a kowace rana a Najeriya, yana mai jaddada kalubalen da ke cikin yawan mutuwar mata da kananan yara.
An yi amfani da gurbattacen jini a Birtaniya na tsawon shekaru wanda ya jawo mutuwar mutane da dama da kuma yaduwar cututtukan kanjamau da ciwon hanta.
A yayin da duniya ke jimamin mutuwar shugaban Iran, Ebrahim Raisi, a hannu daya kuma, an kwantar da sarkin Saudiya, Salman bin Abdulaziz a asibiti saboda cutar huhu.
Ma'aikatar lafiya a jihar Kano ta bayyana cewa kimanin kaso 28.5 na wadanda ke da shekaru 30 zuwa 79 na dauke da cutar hawan jini. Cutar ka iya jawo ciwon koda.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kwara ta cafke likita da kuma masu taimaka masa guda hudu kan zargin batar da mahaifa da kuma cibiyar jariri a jihar bayan haihuwarsa.
Kiwon Lafiya
Samu kari