Labaran garkuwa da mutane
Wasu mahara da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun sace shugaban APC na gunduma ta 5 Ifon a ƙaramar hukumar Ose ta jihar Ondo, sun nemi fansar N100m.
Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ba iyalan limamin Zamfara da aka kashe a Maru N5m da kayan abinci. Sarkin Maru ya yaba da ta'aziyyar Alkali Salihu Sulaiman.
'Yan sanda sun cafke wata dalibar jami'ar Ekiti bisa zargin yin garkuwa da kanta domin ta sha soyayya da saurayinta. Kwamishinan 'yan sanda ya ce za a kai ta kotu.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa DSS kan kama masu garkuwar da suka sace yarinya mai shekara 1 suka wurga ta rijiya bayan karbar kudin fansa.
Wasu mahara da ake zargin ƴan fashin teku ne sun farmaki jiragen ruwa guda 3, sun sace fasinjoji 13 a yankin karamar hukumar Okrika a jihar Ribas jiya Talata.
Shugaban ƙungiyar ɗalibai ta Najeriya (NANS), Atiku Abubakar Isah, ya nemi afuwar ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu da ministan matasa kan kazafin da ya masu.
'Yan bindiga sun kashe limamin garin Maru a jihar Zamfara, Alkali Salihu Suleiman. Sun kashe limamin ne a watan Ramadan tare da 'ya'yansa a cikin daji.
Wasu 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa ne sun sace matar wani basarake a jihar Kaduna. An kashe daya daga cikin wandanda suke je ceto matar sarkin a daji.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana cewa za a yanke hukuncin kisa ga duk wani mai garkuwa da mutane da aka samu da aikata laifin a jihar.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari