Labaran garkuwa da mutane
Asirin wata matar aure ya tonu bayan ta yi garkuwa da kanta tare da karbar kudin fansa N2m daga mijinta tare da raba kudin da saurayinta a Abuja.
'Yan bindigar sun kai farmaki garin Ɓaure da ke ƙaramar hukumar Gusau, jihar Zamfara a yammacin ranar Talata, lokacin da al'ummar garin ke shirin buɗa baki.
An bayyana yadda tsagerun 'yan bindiga suka sako dalibai mata da suka sace a jihar Zamfara. An ruwaito cewa, sun sako su ne bayan shafe wata tara a tsare.
Dakarun ƴan sanda sun damƙe wata mace da ake zargin ta yi garkuwa da kanta da kuma wasu mutane sama da 50 bisa zargin aikata manyan laifuka a Akwa Ibom.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta biya ko sisi ba a matsayin kudin fansa na daliban da 'yan bindiga suka sace a Kaduna.
'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane akalla 61 a wani sabon hari da suka kai garin Buda da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna. Yan sanda ba su ce uffan ba.
Miyagun ƴan bindiga sun buƙaci yan uwan da mutanen da suka sace a Gonin Gora su haɗa Naira tiriliyan 40 a matsayin kuɗin fansa da kuma motoci da babura.
Masu garkuwa da mutane da suka sace almajirai a jihar Sakkwato sun nemi a tattara musu Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa gabanin su sako su.
Wasu ƴan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da mataimakiyar darakta da wani jami'in tsaro a asibitin jami'ar Najeriya da ke Enugu.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari