Kasashen Duniya
A wannan shekarar ta 2024, akalla 369 cikin 2,781 mafi arziki a duniya mata ne, suna da kaso 13.3% na jerin, kuma yawansu ya karu ne daga 337 da aka samu a 2023.
Dattijon da ya fi kowa shekaru a duniya, Juna Vicente Perez Mora ya rasu a jiya Talata 2 ga watan Afrilu da shekaru 114 a kasar Venezuela bayan fama da jinya.
Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya gamu da mummunan hatsarin mota inda ya ci karo da wani direban babbar mota a jiya Alhamis a ƙasar.
An sanar da Bassirou Diomaye Faye wanda ya lashe zaben kasar Senegal inda ya kafa tarihi a matsayin matashi mafi karancin shekaru a zaben da aka gudanar.
Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Pantami da abokinsa, Femi Fani-Kayode sun ziyarci ofishin jakadancin Rasha domin jajanta musu kan harin ta'addanci.
Dan siyasar Senegal mai shekaru 44, Bassirou Diomaye Faye, ya zama zababben shugaban kasa mafi karancin shekaru a nahiyar Afirka. Ya samu kuri'u mafi rinjaye.
An ayyana kasar Finland a matsayin mafi farin ciki a duniya, yayin da Najeriya ta gaza shiga jerin 20 ɗin farko na jadawalin kasashe masu farin ciki a 2024.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya haramta wa ministoci da sauran muƙarraban gwamnati tafiye-tafiye zuwa waje. An dauki matakin ne domin rage kashe kudaden jama'a.
Jami'ar Cape Town ta ci gaba da zama babbar jami'a a Nahiyar Afrika a cikin kuma mai matsayi a jami'o'in duniya na bana kamar yadda Edu Rank ya wallafa.
Kasashen Duniya
Samu kari