Kasar Saudiya
Bayan kwanaki da rasuwarsa, an yi jana'izar fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata a birnin Madina, manyan mutane daga ciki da wajen Najeriya sun halarta.
Rahotanni sun nuna cewa an matsar da jana'izar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga lokacin sallar la'asar zuwa bayan Magriba a masallacin Annabi SAW da ke Madina.
A labarin nan, za a ji cewa an kammala shirin birne Alhaji Aminu Dantata a kokarin cika burinsa na kwantar da shi a kusa da matarsa da ta rasu a 2023.
Alhaji Aliko Dangote ya rako gawar kawunsa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata daga Dubai zuwa Madina. Za a yi jana'izar Dantata a masallacin Annabi SAW.
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya tafi birnin Madina jana'izar Alhaji Aminu Alhassan Dantata bayan rasuwar shi. Dantata ya yi wa Aminu Ado wasiyya.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje sun isa Madina domin jana’izar Aminu Dantata.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa an ɗage jana'izar marigayi Alhaji AminuƊantata zuwa gobe Talata a birnin Madina saboda cika sharuɗdan Saudiyya.
Wakilan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da suka hada da Badaru Abubakar, Aminu Daurawa sun isa Madina jana'izar Aminu Alhassan Dantata a Saudiyya.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jigawa, Umar Namdi, Sanusi II sun tafi Madina jana'izar Dantata tare da tawaga mai karfi da ta hada da tsohon gwamnan Jigawa
Kasar Saudiya
Samu kari