Jihar Kaduna
Malamin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya yi magana kan cece-kucen da ake yi game da yarjejeniyar Samoa da Gwamnatin Tarayya ta sanyawa hannu a Najeriya.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun bi cikin dare sun sace wasu 'yan jarida guda biyu a jihar Kaduna. Miyagun sun sace mutanen ne tare da matansu da 'ya'yansu.
Jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta kada kuri'ar amincewa da gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani. An kada kuri'ar ne a wajen taro wanda El-Rufai ya ki halarta.
Jafaru Sani ya tona yadda Uba Sani yake kaddamar da ayyukan da Nasir El-Rufai ya yi duk da su na kukan ba su san inda aka kai bashin da El-Rufai ya ci ba.
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya sauka a birnin Kaduna domin kaddamar da fara tsarin mayar da waɗaɓda harin bam ya shafa gida a Tudun Biri.
Rundunar sojin Najeriya ta zabi Tudun Biri domin mika tallafin lafiya a jihar Kaduna. Rundunar ta yi haka ne domin gyara alakarta da mutanen garin bayan harin bom.
'Yan bindiga da suka sake alƙali Janet Gimba ta kotun gargajiya a Kaduna sun sake ta. Sun buƙaci kudin fansa N150 miliyan nan da kwana 6 ko su cutar da 'ya'yanta.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya mayar da Cif Jonathan Zamuna zuwa kan karagar mulkinsa bayan da tsohon Gwamna El-Rufai ya tuɓe masa rawaninsa.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda bayan sun yi musu kwanton bauna a jihar Kaduna. Sojojin sun kuma kwato makamai masu yawa.
Jihar Kaduna
Samu kari