Jihar Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana abin da ya sa a gaba a wajen mulki jihar. Uba Sani ya ce burinsa hidimtawa mutanen da suka zabe shi.
Rahotanni sun karyata labarin da ke cewa masarautar Zazzau, karkashin Mai Martaba Ahmad Nuhu Bamalli ta kwace rawanin Magajin Rafin Zazzau, Ango Abdullahi.
Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta nemi Nasir El-Rufai ya nemi afuwa bisa zargin rashin adalci da kuma tsangwamar ɗaliban Shehi wanda ya jefa su a matsala.
’Yan kasuwa a Kaduna sun goyi bayan Uba Sani, Shugaba Boa Tinubu da APC, yayin da suka yi ikirarin cewa sun sha wahalhalu a lokacin mulkin Mallam Nasir El-Rufa’i.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya fadi dalilansa na goyon bayan Olusegun Obasanjo a rigimarsa da Atiku Abubakar yayin da suke mulki.
Kalaman tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai sun rikita siyasar Kaduma, ƴan sanda sun musanta zargin da ya yi cewa sun sace tsohon kwamishinansa.
Hadimin Atiku Abubakar mai suna Abdul Rasheeth, ya caccaki Nasir El-Rufai da ya alakanta kansa da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a hirarsa da yan jarida.
Magoya bayan Nasir El-Rufa'i da masu adawa da shi sun fara musayar yawu a TikTok. Akalla mutane sama da 200,000 su ka fara bibiyar shafin tsohon gwamnan.
EFCC ta gurfanar da wasu mutum hudu a Kaduna bisa damfara da satar N197,750,000. Kotun ta bada umarnin tsare su, tare da dage sauraron belinsu zuwa Maris 17.
Jihar Kaduna
Samu kari