Malamin addinin Musulunci
Jami'an NSCDC sun cafke ɓarawon da ya sharara da sata a masallacin Juma'a na Dakata a jihar Kano. Barawon ya sace kayan wutar sola a masallacin Juma'a.
Sheikh Bello Yabo ya ce kiran Abba tsaya da kafarka zalunci ne. Ya ce bai kamata a raba tsakanin Abba Kabir Yusuf da Rabi'u Musa Kwankwaso ba a Kano.
An yi rashin fitaccen malami kuma shugaban kungiyar JNI, Jafaru Makarfi a jihar Kaduna a daren jiya Asabar 23 ga watan Nuwambar 2024 yana da shekaru 93.
Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya yi magana kan liyafar da Sheikh Kabiru Gombe ya halarta inda ya ce kwata-kwata bai dace malamai su halarci irin wannan wuri ba.
Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da yan Hisbah. Sheikh Aminu Daurawa ya halarci taron yan Hisbah. Sarkin Musulmi ya bukaci ba yan Hisbah cikakken iko domin yin aiki.
Sanata Sunday Katung da ke wakiltar Kaduna ta Kudu ya nada Malam Ilyasu Musa da Fasto Gideon Mutum domin kula da bangaren addinan Musulunci da Kiristanci.
Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya yabawa lauya Abba Hikima da ya maka Ministan Abuja, Nyesom Wike a kotu.
Wata malama mai koyar da ilimin addinin musulunci a wani kauye da ke Kano, Khadija Muhammad ta samu yabo daga jama'a kan sadaukar da kanta tare da ba ta tallafi.
Gwamnatin Neja ta ce za ta mika rahoto ga jami'an tsaro domin su yi bincike kan wani malamin musulunci da ta dakatar bayan zargin sa da yaɗa 'aƙidar Boko Haram'.
Malamin addinin Musulunci
Samu kari