Zanga-zanga: Malamin Musulunci Ya Yi Wa Gwamnati da Matasa Bulaliya a Huduba

Zanga-zanga: Malamin Musulunci Ya Yi Wa Gwamnati da Matasa Bulaliya a Huduba

  • Sheikh Sa’eed Muhammad Yunus ya yi huduba a masallacin Juma'a na ITN a kan halin da Najeriya ta shiga ciki a yanzu
  • Limamin Juma’ar kuma malamin larabci a jami’ar ABU Zariya ya yi gargadi ga matasa game da shirya zanga-zanga
  • Farfesan ya fadawa shugabanni su kawowa al’umma sauki ko kuwa a rasa yadda za a shawo kan matasa a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Sheikh Sa’eed Muhammad Yunus ya yi huduba mai matukar jan hankali a ranar Juma’a, 13 ga watan Muharram 1446.

Malamin ya yi hudubar ne a mimbarin Juma’ar masallacin ITN da ke garin Zariya inda ya fadakar game da cin mutuncin malamai.

Farfesa Sa’eed Muhammad Yunus
Malamin Juma'a, Farfesa Sa’eed Muhammad Yunus ya yi gargadi kan zanga-zanga Hoto: Islamic Trust of Nigeria
Asali: Facebook

Hudubar Sheikh Saeed Yunusa kan zanga-zanga

Kara karanta wannan

Jawabin da ya ceci Sarkin Gaya, Gwamnan Kano ya dawo da shi da aka kirkiro masarautu

Farfesa Sa’eed Muhammad Yunusa ya nusar da musulmai cewa naman malamai guba ne da bai kamata wani ya rika tauna shi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda aka ji limamin ya na bayani kai-tsaye a shafin masallacin a Facebook, ya yi kira da a rika girmama malaman musulunci.

Zanga-zanga: Da gaske an ba malamai kudi?

Hudubar mai taken 'halin da ake ciki a Najeriya' ta koka kan yadda a ke jifan malamai da zargi har ana tuhumarsu da saida addini.

Malamin ya kuma kare malaman da su ka je Abuja domin ganawa da gwamnatin tarayya, ya karyata cewa an biya su miliyoyin kudi.

Rade-radi na yawo cewa wasu malamai sun karbi kudi da nufin hana matasa yin zanga-zangar da ake niyya a watan Agustan nan.

Malami ya haska illar zanga-zanga

Sa’eed Yunus ya kuma ja hankalin matasa game da sharrin zanga-zanga, ya dauko tarihi tun daga lokacin kisan Sayyidina Usman RA.

Kara karanta wannan

Malami ya kasafta yadda karamin ma’aikaci zai karar da albashin N70, 000 a abinci a wata

Limamin ya ce kasashe irinsu Sudan da Libya sun fara ne da zanga-zangar lumana, amma yau sun zama abin tausayi cike da nadama.

A cewarsa bai dace Najeriya da ke fama da matsalolin ruwa da wuta ta shiga abin da zai iya jagwalgwala halin da jama’a su ke ciki ba.

Huduba: Malami ya tabo gwamnati da shugabanni

Kafin ya sauka daga mimbari, Farfesa Sa’eed Yunus ya yi kira da babban murya da gwamnati ta guji abin da zai jawo fushin matasa.

Farfesan ya koka kan kuncin rayuwar da aka shiga a yau, yake cewa idan ta kama a dawo da tallafin man fetur domin a samu sa’ida.

A maimakon fito da hanyoyin taimakon talaka, limamin ya zargi masu mulki da sace dukiyar al’umma, ya na tsoron hakan ya jawo bore.

Har ila yau, Sheikh Yunus ya yi Allah-wadai da yadda ake tsige wadanda ake ji su na fadan gaskiya a maimakon a dauki shawararsu.

Kara karanta wannan

Kalamai a kan gwamnatin da suka tsumbula Sanata Ndume cikin ruwan zafi a APC da majalisa

Shehin malami ya kare shehunnai

Rahoto ya zo kafin nan cewa Sheikh Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya yi magana mai kaushi a kan masu cin mutuncin malamai

Shehin malamin ya yi tir da masu zargin an biya su N16m domin saida ‘yancin al’ummar musulmi, su hana a iya shirya zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng