INEC
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta tantance wasu kungiyoyi 116 na Najeriya da kuma na kasa-da-kasa 28 da za su sanya idanun lura akan babban zaben kasa da zai gudana cikin fadin Najeriya a watan gobe da jibi.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito INEC ta sanar da haka ne a ranar Talata 15 ga watan Janairu yayin da take bayyana jadawalin shirye shiryen zaben 2019 dake dauke da tsare tsaren da ta tanada domin ganin an gudanar da zaben cikin sauki.
A jiya ne dai Dangin Amina Zakari sun fayyace gaskiyar zargin alakar ta da Buhari. Dangin Amina Zakari sun fito sun ce yayar Buhari ta taba aure a gidan mu amma sai dai auren bai dade ba aka samu saki ya shiga.
A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta gabatar da jimilla ta adadin al'ummar kasar nan da suka shirya babban zabe na 2019. Hukumar ta ce 'yan Najeriya 84m ke da rajista ta cancantar kada kuri'u.
Za ku ji cewa Hukumar INEC za ta hada kai da Magu da Hukumar EFCC saboda zaben 2019. Hukumomin EFCC da ICPC masu yaki da barayi a Najeriya sun ce za su idanu a zaben 2019. INEC tace za tayi gaskiya a zaben da za ta shirya a 2019.
Majiyar Legit.com ta ruwaito Sanatan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar ta bakin kaakakinsa, Kayode Odunaro a babban birnin tarayya Abuja, inda yace ba zai zura wasu yan tsirarun Sanatoci su nemi yi ma shugaban kasa
Yayinda zaben 2019 ke gabatowa, hukumar zabe mai zaman kanta ta haramta wa jami’an kasancewa mamba a kungiyoyin WhatsApp. Hukumar zaben ta aika da wata wasika ga dukkanin kwamishinonin zabe 37, inda take sanar masu hukuncin ta.
A yan kwanakin nan ne batun takardar shaidar kammala karatun sakandari na shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya sake tasowa, kuma ya taso tare da gagarumin kuwa daya tarnake farfajiyar siyasar Najeriya a yanzu haka.
LEGIT.com ta ruwaito Sanata Nazif Suleiman ne ya mika ma majalisar cikakken kwaskawararren dokokin, wanda a baya shugaba Buhari yayi watsi dasu, inda yace majalisar ta yi coge akan wasu muhimman abubuwa a wajen shirya dokokin.
INEC
Samu kari