Dage Zabe: INEC ta tabbata zabe ya gudana a mako mai zuwa - Amurka

Dage Zabe: INEC ta tabbata zabe ya gudana a mako mai zuwa - Amurka

- Amurka ta ce tana goyon bayan hukuncin sauran kasashen duniya akan dage zaben Najeriya

- Kasar Amurka ta nemi al'ummar Najeriya da su tabbatar da an gudanar da zabe na gaskiya da adalci

- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta dage babban zabe sa'o'i kadan gabanin gudanar da sa

Mun samu cewa, daga karshe gwamnatin kasar Amurka ta yi furuci na tofa albarkacin bakin ta dangane da dage babban zaben kasa da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yi a jiya Asabar, 16, ga watan Fabrairun 2019.

Gwamnatin kasar Amurka ta ce ta goyi bayan hukuncin da kungiyar kasashen yankin Afirka ta Kudu wato ECOWAS da kuma sauran kasashen duniya masu ruwa da tsaki suka dauka dangane da dag babban zaben kasar nan ta Najeriya a jiya Asabar.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu yayin bayar da sanarwar dage babban zabe
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu yayin bayar da sanarwar dage babban zabe
Asali: UGC

Cikin wata sanarwa a jiya Asabar da ta fito daga ofishin jakadin kasar Amurka da ke Najeriya, ta yi kira ga daukacin al'ummar kasar nan da su dukufa wajen tabbatar da hukumar INEC ta gudanar da tsarkakken zabe na gaski da adalci.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar kasashen duniya masu sanya idanun lura reshen kasar Najeriya ta yi kira na gargadi ga hukumar INEC da tabbatar da gudanar da zaben kasa kamar yadda ta kayyade a sabon jadawalin ta.

Kungiyar ta kuma yi kira ga al'ummar kasar nan da su dauki dangana tare da zama lafiya wajen goyon bayan hukumar INEC yayin da ta ke ci gaba da fafutikar gudanar da zaben kasa bisa tanadin na sabon jadawalin ta.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar ECOWAS da ta bayyana ruwa da tsakin ta bisa jagorancin Ellen Johson Sirleaf, tsohon shugaban kasar Liberia da kuma kungiyar tarayyar Afirka bisa jagorancin Hailemariam Desalengn, tsohon Firai Ministan kasar Habasha.

KARANTA KUMA: Kamfanin Jiragen sama sun yi asarar biliyoyin dukiya sakamakon dage zabe

Sauran kungiyoyin sun hadar da; kungiyar kasashe renon Birtaniya ta Commonwealth bisa jagorancin Dakta Jakaya Kikwete, tsohon shugaban kasar Tanzania, kungiyar Electorate Institute for Sustainable Democracy in Africa bisa jagorancin Rupia Banda, tsohon shugaban kasar Zambia.

Dakta Muhammad Ibn Chambas, jagoran kungiyar masu ruwa da tsaki kan harkokin siyasar Afirka, wakilin majalisar dinkin duniya reshen yankin Afirka ta Kudu da kuma Ambasada Boubakar Adamaou, jagoran kungiyar hadin kan addinin Islama.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng