Amina Zakari ba ta da alakar jini da Shugaban kasa inji Dangin ta
Dangin babbar jami’ar hukumar zaben nan na kasa na INEC watau Amina Zakari wanda har gobe ake ce-ce-ku-ce a game da sabon mukamin da aka ba ta sun fito sun yi magana game da surutun da ake yi.
Dangin wannan Baiwar Allah sun bayyana cewa zargin da ake yi na cewa kwamsihimar hukumar zaben ta na da alaka da shugaban kasa ba gaskiya bane. Wani ‘Dan uwan ta mai suna Isah Zakari, ya bayyana wannan jiya.
Alhaji Isah Zakari yayi kira ga jama’a su shafa masu lafiya su daina yada jita-jita game da ‘Yar uwar ta su. Dangin na ta sun bayyana cewa ana yada wannan rade-radin ne kurum domin a batawa babbar jami’ar zaben suna.
‘Dan uwan ma’aikaciyar ta hukumar INEC ya tabbatar da cewa wata Yayar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta taba aure a gidan Mahaifiyan ita (Hajiya Amina Zakari), sai dai a cewar su, wannan aure bai kai ko ina ba aka rabu.
KU KARANTA: Ba za mu yarda da matsayin da INEC ta ba ‘Yar uwar Buhari ba – PDP
Zakari a jawabin da ya fitar Ranar Litinin, ya bayyana cewa Mahaifiyar Amina Zakari ta tashi ne har kuma tayi wayau a Kano duk da cewa haihuwar Daura ce. Isa Zakari a madadin Dangin jami’ar yace abin ya isa haka nan.
Dangin su ka ce wanda ya fara yin wannan magana ya fito ya janye don haka babu dalilin a cigaba da yada abin da ba gaskiya bane. Dattijon nan na Arewa watau Alhaji Tanko Yakassai shi ne wanda ya fara yin wannan ikirari.
Kwanaki Ayo Fayose ya fito yace Amina Zakari ta ajiye mukamin da aka ba ta saboda gudun kar ayi amfani da ita wajen murde zaben bana. Tsohon gwamnan na Ekiti yace akwai yiwuwar Zakari ta murdewa PDP zaben 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng