Tuna baya: Yadda hukumar INEC ta dage zaben 2011

Tuna baya: Yadda hukumar INEC ta dage zaben 2011

Da yawa daga cikin al'ummar Najeriya sun bayyana fushin su dangane da hukuncin hukumar zabe ta kasa mai zaman wato INEC, na dage babban zaben kujerar shugaban kasa cikin abinda bai wuce sa'o'i goma gabanin gudanar sa.

Ko shakka ba bu ba kansa farau ba domin kuwa hakan ta kasance a manyan zabukan kasar nan biyu da suka gabata na 2015 da kuma mafi bakin cikin aukuwa a shekarar 2011 kamar yadda masu sharhi suka zayyana.

A shekarar 2011, bayan fara gudanar da zabe cikin wasu jihohi da ke fadin kasar nan, hukumar INEC bisa jagorancin shugaban ta na wannan lokaci, Farfesa Attahiru Jega, ta bayar da sanarwa dage babban zaben kasa har zuwa tsawon kwanaki biyu.

Tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega

Tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega
Source: Depositphotos

Tarihi ya tabbatar da cewa, tiryan-tiryan an fara gudanar da zaben kujerar 'yan majalisun tarayya a ranar 2 ga watan Afrilun 2011 cikin wasu jihohin kasar nan da suka hadar da Legas, Kaduna, Kebbi, Delta, Zamfara da kuma Enugu.

Kwatsam ba tare da aune ba shugaban hukumar INEC, Farfesa Jega, ya bayar da sanarwa dage zaben sakamakon wasu dalilai da ya wassafa na rashin rarraba kayayyakin zabe a kan kari cikin wasu yankunan kasar nan.

A yayin zaman kirdado na cikar kwanaki biyu domin gudanar da zaben, hukumar INEC ta sake dage shi zuwa ranar Asabar, 9 ga watan Afrilun 2011, yayin da ta dage zaben kujerar shugaban kasa daga ranar 9 ga wata zuwa 16 ga watan Afrilun 2011.

KARANTA KUMA: Ba na tsoron faduwa zabe - Buhari

Shafin jaridar The Cable gami da waiwaye na manema labarai na jaridar Legit.ng bisa ga madogara ta tarihi, hukumar INEC ta kuma dage zaben kujerar gwamnoni daga ranar 16 zuwa 23 ga watan Afrilun 2011.

Shekaru hudu bayan aukuwar wannan lamari a kasar nan, hukumar INEC bisa jagorancin tsohon shugaban ta Farfesa Jega, ta kuma dage babban zaben kasa na 2015 zuwa tsawon makonni shida bisa ga wassafar dalilan ta na ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram da har ila yau kasar nan ke ci gaba da fuskanta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel