Jihar Kano da Legas na gaba ta fuskar yawan ma su zabe - INEC

Jihar Kano da Legas na gaba ta fuskar yawan ma su zabe - INEC

A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta gabatar da jimilla ta adadin al'ummar kasar nan da suka shiryawa babban zabe na 2019. Hukumar ta ce 'yan Najeriya 84,004,084 ke da rajista ta cancantar kada kuri'u a zaben.

Yayi gabatar da wannan adadi a gaban shugabannin jam'iyyun kasar nan, shugaban hukumar zabe, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce jihar Legas da kuma Kano sun sake kasancewa kan gaba wajen yawan adadin masu zabe a bana.

Cikin fiye da masu zabe miliyan 84, Farfesa Yakubu ya ce, jihar Legas na da masu cancantar zabe miliyan 6.6 yayin da jihar Kano ka bi mata baya da masu zabe miliyan 5.5. Ya ce jihohin biyu sun sake yiwa sauran jihohin Najeriya zarra ta wannan fuska kamar yadda ta kasance a zaben 2015.

Shugaban hukumar zabe; Farfesa Mahmoud Yakubu

Shugaban hukumar zabe; Farfesa Mahmoud Yakubu
Source: Depositphotos

Tarihi ya bayyana cewa, a shekarar 2015, jihar Legas ta samar da adadin masu zabe miliyan 5.8 yayin da jihar Kano ta bayar gudunmuwar masu zabe miliyan 5.0 kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Shugaban hukumar ya kuma bayyana takaicin sa dangane da kawowa yanzu akwai tarin katin zabe da mamallakan su suka zaga karba a hannun hukumar da ya kasance babban makami a gare su yayin babban zabe.

KARANTA KUMA: Na yi alkawarin habaka nagartar dakarun tsaro - Buhari

Ko shakka ba bu hukumar ta kayyade cewa, za a gudanar da zaben kujerar shugaban kasa da kuma na 'yan majalisar tarayya a ranar 16 ga watan Fabrairu, inda za a gudanar da zaben gwamnonin da kuma na 'yan majalisun dokoki na jiha a ranar 2 ga watan Maris na shekarar nan.

Cikin wani rahoton jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai kamata a sake zaben gwamnoni da ba su tsinanawa al'ummar jihar su aikin komai ba tsawon shekaru hudu a karagar mulki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel