Dage Zabe: Jami'an tsaro za su fi kowa shan wahala - Bincike

Dage Zabe: Jami'an tsaro za su fi kowa shan wahala - Bincike

A ranar Asabar, 16, ga watan Fabrairun 2019, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta dage babban zaben kasa na shugaban kasa da kuma na 'yan majalisar tarayya zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu na shekarar da muke ciki.

A yayin da al'ummar kasar nan da dama suka fusata dangane da wannan lamari na bazata, wani bincike da masana suka gudanar ya tabbatar da cewa, jami'an tsaro za su fuskanci babban kalubale na tagayyara a sakamakon dage babban zaben na kasa.

Dage Zabe: Jami'an tsaro za su fi kowa shan wahala - Bincike
Dage Zabe: Jami'an tsaro za su fi kowa shan wahala - Bincike
Asali: UGC

Kwararrun binciken cikin wata hira da manema labarai a jihar Legas, sun bayar da tabbacin su da cewa jami'an tsaro da aka watsa cikin lunguna da sakonni na kasar nan domin sauke nauyin da rataya a wuyan su za su fuskanci kalubale na wahala sakamakon dage babban zabe.

Cikin ire-iren hali na tagayyara da masu binciken suka wassafa sun hadar da batar da kudade doriya akan wadanda ya kamatu jami'an tsaro su batar sakamakon rashin yiwuwar zaben yayin da za su ci gaba a wuraren da aka kayyade masu na aiki har zuwa mako na gaba.

KARANTA KUMA: Ba bu wani shiri na tsige shugaban hukumar INEC - Fadar Shugaban kasa

Wani tsohon jami'in tsaro, Mataimakin sufeto janar na 'yan Sanda, Marvel Akpoyibo mai ritaya, ya misalta hukuncin dage babban zaben kasa a matsayin wani lamari na tagayyara da za su fuskanta baya ga zaman kashe wando na ba bu gaira ba bu dalili.

Kazalika wani jami'in tsaro, Roy Okhidievbie, ya ce hukuncin INEC na dage babban zabe ya haddasa tasgaro musamman a tsakanin jami'an tsaro da kuma 'yan siyasa da a halin yanzu dole sai sun sake dabarun su gabanin zaben a mako mai zuwa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel