Sanarwa: Hukumar INEC ta fara daukan ma’aikata, duba yadda ake neman aikin

Sanarwa: Hukumar INEC ta fara daukan ma’aikata, duba yadda ake neman aikin

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta ta sanar da bukatar daukan ma’aikatan wucin gadi da zasu taimaka wajen gudanar da babban zaben gama gari na shekarar 2019 dake tafe a watan Feburairu da watan Maris

Majiyar Legit.ng ta ruwaito INEC ta sanar da haka ne a ranar Talata 15 ga watan Janairu yayin da take bayyana jadawalin shirye shiryen zaben 2019 dake dauke da tsare tsaren da ta tanada domin ganin an gudanar da zaben cikin sauki.

KU KARANTA: Yadda wani Dansanda direban bankaura ya bankade abokinsa Dansanda da mota

Sanarwa: Hukumar INEC ta fara daukan ma’aikata, duba yadda ake neman aikin
Ma'aikatan zabe
Asali: Depositphotos

Haka zalika ko a shafinta na twitter da na yanar gizo, INEC ta bayyana rukunin ma’aikatan da take bukata, daga ciki akwai jami’in kula da akwatin zabe (PO-Presiding Officer), mataimakin jami’in kula da akwati (Assistant Presiding officer-APO).

Sauran sun hada da , jami’in sa ido akan akwatunan zabe (SPO), jami’in kula da rumfunan zabe (Registration Area Center-RAC) da kuma jami’in kula da kayan aiki a rumfuna (Registration Area Technical Support – RATECH).

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, hukumar ta bada damar neman wannan aiki ne ta shafinta na yanar gizo watau https://pres.inecnigeria.org daga ranar Talata 15 ga watan Janairu zuwa Litinin21 ga watan Janairu.

Sai dai duk kokarin da wakilin Legit.ng ya yi na shiga wannan shafin yanar gizo a daren Talata ya ci tura, sakamakon yawan jama’an dake kokarin kaiwa garesa tare da neman wannan aikin, amma akwai wasu hanyoyi guda biyu da za’a iya bi wajen neman aikin nan da suka hada da;

- Sauke takardar neman aikin daga shafin yanar gizon, a cika shi a mika ma ofishin hukumar dake kusa

- Ga daiban makarantun gaba da sakandari, zasu iya mika sunayensu ga hukumar makarantarsu don ta mikasu ga INEC.

Sai dai bincikenmu ya tabbatar da cewar wasu makarantu, jami’o’I da kwalejoji sun kammala tattara sunayen daliban da suka nuna sha’awar yin aikin sun mika ma INEC, sai a tuntubi makarantu don samun karin bayani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng