Batun takardun karatun Buhari ya bar baya da kura: Amma mai kundin tsarin mulki yace?
A yan kwanakin nan ne batun takardar shaidar kammala karatun sakandari na shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya sake tasowa, kuma ya taso tare da gagarumin kuwa daya tarnake farfajiyar siyasar Najeriya a yanzu haka.
Legit.com ta ruwaito tun a gabanin zaben 2015 ne aka fara wannan batu, inda Buhari ya aika ma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, da takardar rantsuwa daga Kotu dake nuna cewa ya yi karatun sakandari, a maimakon takardunsa, wanda yace suna hannun hukumar Sojin Najeriya.
KU KARANTA: Uwargidar shugaban kasa ta karrama wani jajirtaccen Dansandan Najeriya
A yanzu ma da zaben 2019 ke karatowa, magauta sun nemi Buhari ya bayyana takardunsa na kammala karatu, sai dai fadar shugaban kasa ta bayyana cewa takardun Buhari na hannun hukumar Soji, amma kuma ita hukumar tace takardun sun bace bat!
Da wannan ne muka yi duba ga kundin dokokin Najeriya, wanda sune madubi ga duk wasu bahallatsa, sai dai wannan bincike ya gano wasu abubuwan daure kai game da ka’idojin tsayawa takarar shugaban kasa, wanda Buhari zai iya sha da su.
Sashi na 131, sakin layi na (d) ya bayyana sharudda ko ka’idojin da take bukatar duk wani mai nufin zama shugaban kasar Najeriya ya cika kafin ya tsaya takara
- Ya kasance an haifeshi a Najeriya
- Ya kasance ya kai shekaru 40
- Ya kasance yana da jam’iyya, kuma jam’iyyar ta gabatar da shi
- Ya kasance ya kai matakin karatu na Satifiket
Sai da sashi na 128 na kundin tsarin mulki ya yi Karin haske akan dokar take nufi da ‘Matakin karatu na Satifiket’ ko makamancinsa, inda tace;
- Satifiket na kamala karatun Sakandari, ko Grade II da makamancinsa
- Samun Ilimi har zuwa matakin Sakandari
- Shaidar kammal ilimin firamari a aji 6
- Aikin gwamnati ko a waninsa na tsawon shekara 10
- Halartar kwasa kwasai da samun horo a cibiyoyi na shekara 1
- Kwarewa wajen rubutu, karatu da fahimtar harshen Turanci
Duba da wannan a iya fahimtar cewa ba lallai bane duk mai takarar shugaban kasa ya mika ma INEC takardar shaidar kamala karatun sakandari, sai dai idan har ya kai matakin ilimin sakandari ma ya wadatar.
Za’a iya fahimtar haka a hukuncin da babbar kotun jahar Osun ta yanke a shari’ar dan takarar gwamnan jahar Osun a jam’iyyar PDP, Sanata Adeleke a shekarar 2018, ko kuma hukuncin kotun daukaka kara a shari’ar Bayo Vs Njidda (2004).
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng