Kira da babban murya: Saura kwana 1 rak a rufe amsan katin zabe

Kira da babban murya: Saura kwana 1 rak a rufe amsan katin zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanar da ranar Juma’a, 8 ga watan Feburairu a ranar da za ta rufe bayar da katin zabe ga jama’an da zasu kada kuri’a a babban zaben watan Feburairu dake karatowa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar INEC ta ce ba zata sake baiwa kowa katin zabe daga ranar Juma’a bane saboda ta samu damar gudanar da sauran shirye shiryen da suka shafi zaben 2019 don haka take kira ga duk wanda yayi rajista daya garzaya ofishin INEC mafi kusa don karbar katinsa.

KU KARANTA: Maza kwaya, mata kwaya: An tura wani kwamishinan Yansanda mai abin mamaki jahar Kano

Kira da babban murya: Saura kwana 1 rak a rufe amsan katin zabe

katin zabe
Source: Depositphotos

“Muna kira ga duk wanda yayi rajistan zabe daya garzaya ofishin INEC mafi kusa don karban katin zabensa da kansa, mun yi haka ne domin tabbatar da babu wani katin zabe daya shiga hannun da ba na mai shi ba.” Inji shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.

A ranar Asabar, 16 ga watan Feburairu ne hukumar zabe mai zaman kanta za ta gudanar da zaben shugaban kasa da nay an majalisun wakilai da na dattawa, sai kuma a ranar 2 ga watan Maris a gudanar da zaben gwamnoni da nay an majalisun jihohi.

A cikin wani bayani da hukumar zabe ta fitar ta bayyana cewa akwai akalla mutane miliyan tamanin da hudu, 84,000,000 da suka yi rajistan zabe, amma kuma har yanzu akwai miliyoyin jama’a da basu karbi katukan nasu ba.

Ga wata hanyar da INEC ta bayar domin gano inda katin zabe yake a shafin yanar gizonta, kayi amfani da lambobin rumfar zabenka da aka rubuta a katinka na wucin gadi wanda ake kira Pollint Unit (PU), sai ka rubuta lambar a sashin neme neme na shafin, zai nuna maka inda katinka yake, daga nan sai a garzaya a karba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel